Ɗan wasan gaba na Manchester United Jadon Sancho ba zai ci gaba da atasaye da sauran 'yan wasan kulob ɗin ba har sai an sasanta rikici tsakaninsa da koci Erik ten Hag.
Ten Hag bai saka Sancho cikin tawagarsa da ta sha kashi a hannun Arsenal ba a farkon wannan watan, yana mai cewa ƙwazonsa bai kai wanda ake nema ba a wurin atasaye.
Sancho mai shekara 23 ya yi watsi da kalaman kocin, inda ya ce "kawai ɗora masa laifi ake yi tsawon lokaci".
Cikin wata sanarwa, United ta ce Sancho zai ci gaba da "atasaye na musamman shi kaɗai ba tare da sauran 'yan wasa ba".
Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne "har sai an kammala binciken ladaftarwa".
Lamarin Sancho na faruwa ne cikin mako ɗaya da wani ɗan wasan na United, Antony, ya fice daga sansaninta sakamakon zargin cin zarafi da tsohuwar abokiyar zamansa ta yi masa.
A shekarar 2021 Sancho ya koma Man United daga Borussia Dortmund kan fan miliyan 73.
Sai dai bai taɓuka wani abin kirki ba tun bayan komawar tasa, inda ya ci ƙwallo tara kacal da kuma ba da shida a zira a raga cikin wasa 58 da ya buga a Premier League.