Bincike ya tabbatar da samar da ɗan tayin biri da ke dauke da ƙwayoyin halittar dan adam, wanda aka samar a ɗakin gwajin kimiyya.
Binciken wanda tawagar mutanen China da Amurka suka gabatar, ya janyo muhawara kan cewa ko irin wadannan gwaje-gwaje sun dace ko kuma akasin haka.
Masana kimiyya ne suka sanya ƙwayoyin halittar ɗan adam da suke da yiwuwar haɓaka a jiki - kuma aka sanya su a jikin ɗan tayin biri.
An yi ta yin nazari kan yadda ƙwayoyin suka riƙa haɓaka a jikin dan tayin biri har na tsawon kwana 20.
A baya ma an yi wasu gwaje-gwajen a jikin ɗan tayin wasu halittun kamar jikin ɗan tayin tinkiya da na alade.
Farfesa Juan Carlos Izpisua Belmonte na cibiyar Salk da ke Amurka, wanda a 2017 ya jagoranci yadda aka yi dashen ƙwayoyin halittar dan adam a jikin alade a karon farko cikin tarihi, yanzu ma shi ke jagorantar wannan aikin.
Wannan aikin da suke yi wataƙila ya share hanyar matsalar ƙarancin dashen ƙwayoyin halittar dan adam da ake samu, zai kuma iya taimaka wa wajen fahimtar yadda mutum ya samo asali a shekarun baya, in ji shi.
"Yadda ake nazari kan ƙwayoyin halittar zai taimaka sosai wurin binciken da ake ba kawai kan fahimtar rayuwa a baya ba, a'a har da fahimtarta a nan gaba."
Ya kuma ce wannan binciken da aka wallafa a mujallar Cell, bai saɓa da ƙa'idojin da aka shimfida ba a yanzu.
"Muna yin wadannan bincike-binciken ne domin fahimta da kuma haɓaka lafiyar ɗan adam," in ji shi.
'Kalubalen ka'idojin aiki'
Wasu masana kimiyyar sun ja hankali kan gwaje-gwajen, suna cewa yayin da ake lalata wasu 'yan tayi da suke cikin kwanakinsu na 20, wasu kuma na yunƙurin ciyar da ayyukan gaba.
Suna neman a gabatar da muhawara kan tasirin ƙirƙirar halittar wani abu da rabinsa mutum rabinsa dabba.
Da take tsokaci kan binciken, Dr Anna Smajdor ta Jami'ar Gabashin Anglia da ke Norwich, ta ce "Ya matuƙar saɓa wa doka da kuma ƙa'idojin aikin likatanci".
Ta kara da cewa, "Wadanda ke gudanar da binciken sun gaza bayar da wasu alfanu da za a samu ko kuma wasu sabbin damarmaki da binciken zai samar, saboda ba za mu iya tantance ɗan tayin me zamu samar ba, mutum ko kuma dabba, wannan tambaya ce ga kowa."
Farfesa Julian Savulescu na Jami'ar Oxford ya ce wannan binciken zai iya samar da "wasu cututtuka tsakanin mutane da kuma halittun da ake son samarwa.
Kuna iya bin Helen oa shafinta na Twitter.