BBC Hausa of Tuesday, 5 September 2023

Source: BBC

Saudiyya ta dage a kan Salah, Sancho na cikin rashin tabbas

Mohamed Salah Mohamed Salah

Wasu jami’ai daga Saudiyya sun isa Ingila, don gwada sa'ar ƙarshe a ƙoƙarinsu na shawo kan Liverpool ta amince ta sayar da Mohamed Salah a kan fam miliyan 200 kafin ranar Alhamis, akwai imanin cewa ɗan wasan mai shekara 31 ɗan asalin Masar zai yarda ya koma Al-Ittihad. (Mail)

Besiktas na dab da cimma yarjejeniya da ɗan wasan gefe na Arsenal daga ƙasar Ivory Coast, Nicolas Pepe, mai shekara 28 a kan farashi mai rangwame. (90min)

Ɗan wasan gefe a Ingila Jadon Sancho, mai shekara 23, zai iya rasa madafa a Mancheter United a wannan kaka, sai dai fa idan ya kufce ya tafi Saudiyya, a cewar tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Rio Ferdinand. (Telegraph)

Tsohon ɗan wasan bayan Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 37, ya yi watsi da tayin ƙarshe da aka gabatar masa daga Manchester United, kafin ya cimma yarjejeniyar koma wa Sevilla. (Sun)

Ana ra san, West Ham za ta cimma yarjejeniyar gajeren lokaci da ɗan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 30, Jesse Lingard, yayin da aka tafi hutu a gasannin duniya. (Mail)

Al-Ettifaq na fatan sayen ɗan wasan Everton daga ƙasar Jamaica, Demarai Gray, mai shekara 27, daidai lokacin da ɗan ƙwallon ya matsu ya bar filin wasa na Goodison Park. (90min)

Kyaftin ɗin Newcastle United, Jamaal Lascelles, mai shekara 29, ya kasance wanda ƙungiyar Al-Shabab ta Saudiyya ke hari a yanzu. Matsayin ɗan wasan bayan na Ingila ya ragu a ƙungiyar, kuma ana jin zai iya kwaɗayin tayin da aka yi masa na kasancewa a sahun manyan ‘yan ƙwallon kulob ɗin na Saudiyya. (TEAMtalk)

Anderlecht na farautar Kasper Schmeichel, mai shekara 36, bayan ya bar Nice a makon jiya. Ƙungiyoyi irinsu Chelsea da Nottingham Forest da Brentford na zawarcin golan na ƙasar Denmark a wannan bazara.

Manchester United na ƙoƙarin ganin ta sayar da ɗan wasanta mai shekara 29 ɗan asalin ƙasar Ivory Coast, Eric Bailly da kuma ɗan ƙwallon da ke buga mata a tsakiya Donny van de Beek, mai shekara 26, kafin a rufe kasuwar hada-hadar 'yan wasa ta ƙasar Saudiyya ranar Alhamis. (Sun)

Mai tsaron raga a Tottenham ɗan ƙasar Faransa, Hugo Lloris, mai shekara 36, zai ci gaba da zama a ƙungiyar, aƙalla har ƙarshen Janairu, bayan ya yi watsi da tayin da aka rinƙa gabatar masa a tsawon lokacin bazara. (Standard)