BBC Hausa of Sunday, 18 June 2023

Source: BBC

Shugaba Putin ya ce hare-haren martanin Ukraine ba sa nasara a kan Rasha

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha Shugaba Vladimir Putin, na Rasha

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha ya ce hare-haren martani da Ukraine ke kai wa ba sa yin nasara, hasali ma sojojin Ukraine na asara sosai.

Da yake magana a wani taron manema labarai na 'yan jarida da ke aika rahotanni kan yaki, ya ce asarar da Ukraine din ke tafkawa ta kama hanyar kaiwa wani mummunan mataki.

To sai dai kuma babu wanda ya tabbatar da wannan ikirarin na Mista Putin, wanda kuma Shugaba Zelensky na Ukraine din ya musanta cewa ba sa samun nasara.

A yayin taron manema labaran Shugaban Putin wanda ya yi ikirarin cewa Ukraine ba ta samun nasara a martanin da take kaiwa a yakin da kasarsa ke yi da ita, yana furta kalaman ne kawai ba tare da gabatar da wata sheda ba, inda har ya ce Ukrane ta yi asarar manyan motocin yaki na igwa sama da 160, yayin da ita kuwa kasarsa ya ce 54 kawai ta rasa .

Haka kuma ya nuna cewa asarar dakarun da Ukraine ke yi ta ninka wadda Rasha ta yi sau goma, yana mai kafewa da kuma jaddada cewa ba wani bangare da Kyiv ta yi nasara a yakin.

Sai dai wani jami’in Amurka wanda ya nemi kada a bayyana sunansa ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa, bayanan na Putin ba daidai suke ba, ya kuma yi gargadi da kada a dauki kalaman na Moscow da muhimmanci.

Haka shi ma Shugaba Zelensky na Ukraine wanda ya yi watsi da kalaman na Mista Putin a jawabin da ya saba gabatarwa ta bidiyo da daddare, ya ce martanin nasu na samun nasara, inda yake mika godiya ga dakarun kasarsa kan duk wani taki na kasar da ya ce sun kwato daga ma su mamayar tasu.

Babban kwamandan sojin Ukraine din Valery Zaluzhny, ya jaddada kalaman na Shugaba Zelensky, inda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Telegram cewa suna ganin tasiri da nasara a hare-haren kuma ya ce suna aiwatar da tsare-tsarensu kamar yadda suke, inda suke yin gaba-gaba.

Ukraine dai a hare-haren martanin na tun da farko ta samu galaba a gabashin Donetsk.

Haka kuma Shugaba Zelensky ya ce suna samun nasara inda suke matsawa a Bakhmut.

Sai dai yanayin ba a fayyace yake ba kamar dai yadda Ukraine din ke ikirarin nasarar da ta bayyana a farkon makon nan.

A ranar Talata sojin Ukraine sun bai wa BBC damar shiga wasu daga cikin yankunan gabashin Donetsk inda suka kwato aka kuma kafa tutar Ukraine.

Yankuna da dama ba kowa kuma akwai alamun dakarun Rashar sun ja baya.

Shugaban kungiyar tsaro ta Nato Jens Stoltenberg, ya ce duk da cewa zai zama wani hanzari a ce an yi galaba a kan Rashawan, to amma a bayyane take cewa an kora sojojin mamayen baya.