Shugaban ƙasar, Kenya William Ruto ya roƙi afuwar al’ummar ƙasar kan mace-mace wasu mabiya addinin kirista da ke azumin ‘ganin Yesu almasihu.’
Inda ya ce akwai sakacin gwamnati kan faruwar lamarin.
Ya zuwa yanzu an gano gawarwaki sama da 200 a dajin Shakahola, inda aka yi amannar cewa an tilasta wa mabiya yin azumi na tsawon lokaci kan cewa za su haɗu da Yesu.
Har yanzu akwai mutum 600 waɗanda ba a san inda suke ba.
Mr Ruto a wata tattaunawa da aka yaɗa ta kafar talabijin ta ƙasar ya ce “Na ɗauki alhakin duk abin da ya faru a matsayina na shugaban ƙasa, bai kamata a ce an bari wannan mace-mace sun faru ba. Saboda haka ina neman afuwar ku.”
Ya ɗora laifi a kan jami’an ƴan sanda da na masu tsaron ciki na ƙasar bisa gazawar su wajen gano ayyukan ƙungiyar a kan lokaci.
Ya ce duk wani jami’i da alhakin hakan ya rataya a kansa zai bayar da bahasi kan faruwar lamarin.
Ruto ya kuma sha alwashin ganin ba a sake samun irin hakan ba a nan gaba.
Yanzu haka jagoran cocin da ake zargi da haddasa mace-macen, Paul Nthenge Mackenzie na hannun jami’an tsaro, inda ake yin bincike kan lamarin.
Tuni aka gurfanar da shi a gaban kotu.
An ba da rahoton cewa Fasto Paul Nthenge Mackenzie ya rufe cocinsa mai suna Good News International Church, shekara huɗu da ta wuce bayan ta shafe kusan shekara ashirin tana aiki.
Sai dai BBC ta bankaɗo ɗaruruwan wa'azozinsa da har yanzu suna nan, ana samun su a intanet, wasu ma ga alama an naɗe su bayan wancan lokaci.
Fasto Mackenzie yana gabatar da wa'azinsa ga ɗumbin masu ibada da suka yi dandazo don jin bayanansa a kan tashin duniya.
"Mun kusa cin yaƙi… Kada wanda ya waiwaya…. mun kusa kai wa gaɓa," abin da aka rubuta ke nan a kan wani ƙyalle da ya ratsa allon bidiyon.
An yi wa wani rukunin bidiyo a tashar cocinsa da ke dandalin Youtube taken: "Yara Lokaci Ya Zo Ƙarshe" inda suke nuna ayarin wasu yara suna gabatar da saƙonni a cikin ƙyamara.