Rundunar sojan Najeriya ta ce tana bincike game da rahotannin da ke cewa an kashe shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.
Ya zuwa yanzu ba a san inda Shekau yake ba tun bayan samun rahotannin da ke cewa ya mutu sakamakon wata fafatawa tsakanin dakarunsa da kuma na ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram.
Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Mohammed Yerima, ya faɗa wa BBC cewa suna bincike kan lamarin amma ba za su ce komai har sai sun samu cikakkiyar hujja game da mutuwar tasa.
Wata kafar labarai mai majiya daga hukumomin tsaro ce ta fara ruwaito mutuwar ta Shekau a faɗan da ya ɓarke a Dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
'Yan Najeriya da dama na murna da labarin mutuwar musamman a shafukan sada zumunta.
Ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun sha fafatawa kan iko da wasu yankuna, a cewar kamfanin labarai na AFP sai dai da alama ISWAP ta fi ƙarfin iko inda ta ke kai munanan hare-hare kan sojoji.
An sha bayyana kisan Abubakar Shekau a baya amma yana fitowa ya ƙaryata, sai dai wannan ne karon farko da rahotanni ke cewa mayaƙan wata ƙungiya ne suka kashe shi ba jami'an tsaro ba.
Shekau ya zama shugaban kungiyar ne bayan da ƴan sanda suka kashe Muhammad Yusuf a 2009, wanda shi ne asalin wanda ya kafa ƙungiyar.
Tun bayan nan an kashe mutum 40,000 yayin da sama da miliyan biyu suka tsere daga muhallansu a ta da ƙayar bayan a arewa maso gabashin Najeriya.
Kawo yanzu kungiyar ISWAP da Barnawi ke jagoranta ba ta ce komai ba kan mutuwar Shekau, kazalika ita ƙungiyar Boko Haram wato ɓangaren Shekau.
Mai bincike kan kungiyoyin masu ikirarin jihadi a cibiyar Tony Blair Institute da ke London, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce ba abun mamaki ba ne idan aka tabbatar da mutuwar Abubuakar Shekau.
"Kusan shekaru huɗu kenan ana gwabza faɗa tsakanin ISWAP da Boko haram don sun kashe kwamandojijin juna ɗaruruwa. Akwai lokacin ma da suka kashe kwamandoji sama da 200 a tsakaninsu" a cewar Bukarti.
Ya ce a irin wannan faɗan ne kuma aka kashe Mamman Nur, na hannun daman Muhammad Yusuf wanda kusan tare ma suka kafa ƙungiyar Boko Haram.
Barista Bukarti ya ce dole jami'an tsaro a Najeriya su zama cikin shirin ko-ta-kwana saboda faɗan an iya kazanta idan aka tabbatar da cewa ISWAP ta kashe Shekau.
"Haka kuma, idan abokan gabarka biyu suna faɗa kai kuma ka samu dama ka je kai masu rubdugu, sai ka yi masu kwab ɗaya kenan. Mai yiwuwa kuma wannan faɗan ya ƙare yanzu, ƙungiyoyin biyu suna iya haɗa kansu su ƙara ƙarfi," in ji Bukarti.
Barista Bukarti ya ce a iya bincikensa, yana ganin akwai dalilai masu ƙarfi da ke nuna cewa Abubakar Shekau ya mutu amma duka ɓangarorin biyu ba su ce komai ba kawo yanzu.