Sifaniya ta kori Jorge Vilda, kociyan tawagar matan kasar da suka lashe kofin duniya, bayan takaddama da ta shafi shugaba, Luis Rubiales.
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Rubiales ya sumbaci Jenni Hermoso a lebe lokacin da ake karrama 'yan kwallon a Australia.
Tuni mataimakan, Vilda suka yi ritaya da 'yan wasa 81 da suka ce sun daina buga wasa idan ba a kori shugaban hukumar kwallon kafar ba.
Rubiales bai yadda ya yi murabus ba, amma dai hukumar kwallon kafar ta duniya, Fifa ta dakatar da shi.
Koda yake hukumar kwallon kafar Sifaniya ba ta bayar da dalilin da ya sa ta kori koci, Vilda ba.
An ga kocin yana tafa wa Rubiales a babban taron hukumar kwallon kafar Sifaniya a cikin Agusta - lokacin da Rubiales ya ce ba zai yi murabus ba, ya kara da ceawr zai tsawaita kwanttiragin Vilda - tun daga lokacin ake caccakar kociyan.
Vilda, wanda yake kan aikin tun 2015 ya fuskanci kalubale a cikin Satumbar 2022, bayan da 'yan wasa 15 suka ce ba za su buga tamaula ba karkashin Vilda.
Daga 'yan wasa 15 uku daga ciki suka ki bugawa kasar tamaula daga baya aka rarrashe su, wadanda suka yi korafi kan salon horarwar Vilda da rashin shiri a kan kari.
A watan jiya Sifaniya ta ci Ingila 1-0 a wasan karshe a gasar kofin duniya a Sydney a Australia.
Vilda ya ja ragamar wasa 108 da cin karawa 75 da kai wa kwata fainal a gasar nahiyar Turai a kwallon mata a 2017 da kuma 2022.