Dandalin zumunta na TikTok ya ƙara yawan adadin shekarun da ya ƙayyade wa yara kafin su iya yaɗa bidiyo kai-tsaye a dandalin daga 16 zuwa 18 daga watan Nuwamba mai zuwa. Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano yadda ɗaruruwan yara ke yaɗa bidiyon kansu da kansu kai-tsaye a sansanonin 'yan gudun hijira daga ƙasar Syria, inda suke barar taimako. Wasu daga cikinsu kan samu kusan dala 1,000 duk awa ɗaya - amma bayan sun karɓi kuɗin sai TikTok ya zare kusan kashi 70 cikin 100 na kuɗin. Nan gaba, baligai ne kaɗai za su iya "tura barar neman taimako ko kuma samun damar shiga wajen samun kuɗi," in ji TikTok. "A 'yan kwanaki masu zuwa kuma, zai ƙyale baligai kaɗai su yi bidiyon kai-tsaye." Ba a san ta yadda TikTok zai aiwatar da wannan sabuwar doka ba. Sai dai kamfanin Meta - wanda ya mallaki Facebook da Instagram - da Google, wanda ya mallaki YouTube, sun ƙayyade shekara 13 ga yara kafin su yaɗa bidiyo na kai-tsaye amma sun bai wa masu wallafa bidiyo damar saka sharaɗin shekaru ga duk wanda zai kalli bidiyonsu. Kyauta ta hanyar latironi Tsawon wata biyar, sashen binciken gaskiya na BBC, sashen BBC Arabic da sashen BBC Eye sun bi diddigin shafukan TikTok fiye da 300 da ke yaɗa bidiyo kai-tsaye daga arewa maso yammacin Syria. Dokokin TikTok sun ce kar mutum ya nemi a ba shi wata kyauta kuma "wajibi ne ya guji cutarwa ko yi wa ƙananan yara ƙeta" a kan dandalin. Lokacin da BBC News ta yi amfani da maɓallin kai rahoto na cikin dandalin don miƙa rahoto kan shafuka 30 da ke nuna ƙananan yara na bara, Tik-Tok ya ce ba a karya dokarsa ba a shafukan. Dandalin ya ce ba ya ƙyale irin waɗannan bidiyon kuma kamashon da ya samu daga wajensu ya yi ƙasa da kashi 70 cikin 100 sosai, amma har yanzu bai bayyaan adadin ba.