BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

Tafiyar Fabinho Saudiyya na neman rugujewa saboda karnuka, Tottenham da Kane saura ƙiris

Harry Kane Harry Kane

An gaya wa shugaban Tottenham Daniel Levy cewa dole ne ya sayar da Harry Kane a bazaran nan idan ba zai iya shawo kan dan wasan na Ingila ya kulla sabon kwantiragin ci gaba da zama a kungiyar ba. (Telegraph)

Wannan labari na bai wa Tottenham wa'adi ya sa Manchester United ta sake zama cikin shirin sayen Kane. (Mirror)

Ita kuwa Bayern Munich wadda aka ki yarda da tayin da ta yi wa dan wasan biyu, tana shirin gabatar da tayi na uku. (Mail)

A shirye Bayern din take ta bai wa Kane kwantiragi mai tsawo na shekara hudu ko ma biyar. (Bild)

Kamar yadda shafin BBC kan kasuwar 'yan wasan kwallon kafa a Turai ya ruwaito.

Tafiyar Fabinho Al-Ittihad ta Saudiyya daga Liverpool tana kasa tana dabo, saboda dan wasan na Brazil na son samun tabbacin tafiya kasar da karnukansa biyu. (Express)

Chelsea ta gabatar da bukatarta ta sayen dan wasan Crystal Palace, Michael Olise kuma tuni daman dan wasan na gaba na gefe, na Faransa asalin Najeriya mai shekara 21, ya kulla yarjejeniya ta baka da Blues din. (RMC Sport )

Ita ma Manchester City tana sha'awar sayen Olisen, wanda ke tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Faransa, wanda yarjejeniyarsa da Palace ta tanadi sayar da shi a kan kusan Fam miliyan 35 ga mai so. (Fabrizio Romano)

Al-Hilal za ta gabatar da tayin Yuro miliyan 200 (£173m) a kan Kylian Mbappe kuma ta yi wa dan wasan na Faransa tayin kwantiragin shekara biyu da albashin Yuro miliyan 200 a duk shekara, watakila da kuma damar sakinsa bayan shekara daya, domin tafiya Real Madrid kawai idan yana so. (Tancredi Palmeri)

Chelsea ta fara kosawa da Romelu Lukaku, saboda dan wasan na Belgium ba ya son tafiya Saudiyya, inda yake jiran wata kungiya ta Turai ta dauke shi. (Gazzetta dello Sport)

Dan gaban Atalanta na kasar Denmark Rasmus Hojlund, yana son a kammala maganar tafiyarsa Manchester United zuwa karshen watan nan na Yuli kasancewar tuni sun cimma yarjejeniya ta baka a tsakaninsu. (Teamtalk)

Wilfried Zaha, zai tafi Galatasaray a kyauta bayan da kwantiraginsa da Crystal Palace ya kare. (Guardian)

Kociyan Fulham Marco Silva ya yi watsi da tayin Fam miliyan 40 da kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya ta yi masa, inda ya zabi ci gaba da zama a kungiyar ta Ingila. (Telegraph)

Chelsea ta sake komawa tattaunawa da hukumar gasar kwararru ta Saudiyya (Pro League) a kan sayar da dan wasan Moroko Hakim Ziyech. (Teamtalk)

Dan wasan gaba na gefe, Callum Hudson, dan Ingila mai shekara 22, na dab da sake hadewa da tsohon kociyansa a Chelsea Maurizio Sarri a Lazio. (Gazzetta dello Sport)

Sai dai kuma Fulham na kokarin ganin ta kasa Lazio ta saye Hudson-Odoi din daga Chelsea. (Nicolo Schira)

Haka kuma Fulham din a shirye take ta biya Fam miliyan 7 a kan Demarai Gray, na Jamaica, wanda Everton ke son sayar da shi. (Sun)

Har-wa-yau Fulham din kuma t yi watsi da tayin Fam miliyan 50 da West Ham ta gabatar mata a kan dan wasan tsakiya na Portugal Joao Palhinha. (90min)

To amma kuma West Ham din tana da kwarin gwiwa cewa Ajax za ta sayar mata da dan wasan tsakiya Edson Alvarez, dan Mexico mai shekara 25 a kan wajen Fam miliyan 40 a bazaran nan. (Football Insider)

Atletico Madrid ta tuntubi Paris St-Germain domin sayar mata da dan wasan tsakiya dan Italiya Marco Verratti, amma kuma Liverpool ma na sonshi, saboda haka dan wasan tsakiya na Tottenham Pierre-Emile Hojbjerg, na Denmark mai shekara 27, na daya daga cikin wadanda Atletico za ta nema idan ta rasa Verratti. (Marca)

Watakila dan wasan gaba Gianluca Scamacca, dan Italiya mai shekara 24, ya koma Roma idan har West Ham ta sayi Divock Origi, na Belgium daga AC Milan, bayan da tattaunawa da Chelsea a kan dan wasan gaba na Albania Armando Broja, mai shekara 21, ta wargaje. (Gazetta dello Sport)

Bayan barin Liverpool a karshen kwantiraginsa tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Alex Oxlade-Chamberlain, na samun gayyata daga Saudi Arabia da Besiktas da Brentford. (Mirror)

Ousmane Dembele, ya yi watsi da tayin kwantiragin shekara biyar, tare da albashin Fam miliyan 35 a duk shekara daga kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya, inda ya zabi ya ci gaba da zama a Barcelona, da ragowar shekara daya a kwantiraginsa. (Foot Mercato)

Dan wasan tsakiya na Austria Marcel Sabitzer ya fi son tafiya Borussia Dortmund a bazaran nan bayan zaman aron da ya yi a Man United daga Bayern Munich a kakar da ta gabata. (Kicker).

Duka wadannan bayanai kamar yadda shafin BBC na kasuwar 'yan wasan kwallon kafa ya ruwaito ne.