BBC Hausa of Tuesday, 19 September 2023

Source: BBC

Takurar da mata ke sha kan sai sun canza sunan mahaifinsu a gidan aure

Hoton alama Hoton alama

Ana samun matan da kan shiga tasku da takura a gidajen aurensu, saboda kawai ba su da ra'ayin cire sunan mahaifinsu, daga sashen sunansu, su sauya da na sabon mijin aurensu.

Akwai mata masu yawa, da ke da ra'ayin canza sunan mahaifansu, tare da maye gurbinsa da sunan sabon angon da suke fatan yin rayuwa ta har abada da shi.

Sai dai, akan samu waɗansu da kan gwammace su ci gaba da amfani da sunan mahaifinsu.

Ko ba komai, suna ganin cire sunan mahaifi daga sashen sunansu tamkar wani yankan baya ne ga iyayen da suka yi ɗawainiya da su tun kafin haihuwa, har zuwa girman da aka ga mace aka aure ta.

Shi kansa sauye-sauyen da matakin zai janyo a yi ga takardun mace, kama daga takardun makaranta da na aiki, har zuwa takardun banki da shaidar zama ɗan ƙasa da sauransu, na iya tsorata wasu.

Amma rashin amincewa da buƙatar canzawar, a wasu lokuta, kan jefa wasu matan cikin tasku da fuskantar tsangwama a wajen mazajensu na aure. Kuma irin wannan ce ta faru da wata amarya, wadda muka sakaya sunanta.

Masana a fannin addini da dokoki sun ce tursasa wa mace ta canza sunan uba da na mijinta, ba shi da wani tushe.

Maryam Usman (ba sunan gaskiya ba ne), ta shaida wa BBC cewa watanni ƙalilan bayan aurensu ne, mijinta ya fara canza mata, ta ce magana ma ba kullum yake yi mata ba.

"Wasu lokuta ma ko abincina ba ya ci."

Ta ce mijinta ya fara yi mata zancen ta canza sunan mahaifinta zuwa nasa, amma sai ta ja hankalinsa a kan wahalar da ke tattare da yin hakan.

Sai dai "Ya ce idan ban yi ba, hakan na nufin tamkar matsayinsa bai kai ba a rayuwata, kuma ba son gaskiya nake (yi) masa ba".

"Har cewa ya yi ƙila ma ƙyamar amfani da sunansa nake, kuma wallahi ba haka ba ne."

'Komai na iya canzawa, amma ban da mahaifi'

Maryam ta ce komai zai iya faruwa, kuma ta san abubuwa na iya canzawa a rayuwa.

A cewarta, abu ɗaya wanda take da yaƙinin ba lallai ne ya canza ba, shi ne sunan mahaifinta kawai, wanda za ta iya dogaro da shi har bayan ranta.

Ta ƙara da cewa mijin nata ya ce matuƙar tana son komai ya daidaita, to, ba shakka ta san me ya kamata ta yi.

"Akwai rashin fahimta ne, shi ya ƙi ya fahimci abin da nake nufi, ni kuma gaskiya zai yi wahala na canza sunan mahaifina" in ji Maryam

Da aka tambaye ta, ko ta faɗa wa mahaifin ta abin da ke faruwa. Sai ta ce a'a, "ai ya yi wuri na fara kai ƙara, sabon aure ne."

"Ni a raina ina jin kamar za mu daidaita da mijina, tun da shi ma bai faɗa wa gidansu halin da muke ciki ba. Ni ma ban faɗa musu ba."

'Musulunci ya hana'

Mun tuntuɓi wani fitaccen malamin addinin Musulunci, don jin ko me addini ya ce game da wannan mas'ala irinta Maryam?

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce addinin Musulunci bai yarda mace ta canza sunan iyayenta don ta musanya da sunan mijinta ba.

"Saboda zai mutu, kuma zai iya sakin ki. To, idan misali mijin ya rasu, za ki yi wani aure, shin za ki ci gaba da amfani da sunansa ne, ko za ki sa sunan miji na gaba?" Malamin ya tambaya.

Ya ce a baya-bayan nan irin wannan dambarwa ta fallasa halin da wata mace ma'aikaciya ke ciki, wadda takardun aikinta suka yi ta nuna yadda ta riƙa canza suna, bayan an yi bincike sai aka fahimci cewa ta yi aure har sau uku.

A cewarsa da sunan mahaifinta take amfani da shi, babu wanda zai gane haka.

Yanzu Nana Aisha (matar Annabi Muhammadu 'S.A.W'), in ji shi, ce mata ake yi, Nana A'isha Bint Abi Bukar Zaujatun Nabi wato Nana Aisha 'Yar Abubakar Matar Annabi. "Haka ake sa mata (suna) uku."

Kamata ya yi a riƙa mutuntawa da martaba juna.

"Cewar an aure ki, ba wai an saye ki ba ne. Ba kuma bauta kika je yi gidan miji ba, kin je aure ne."

A cewarsa, daga cikin mutuntawar shi ne, ki tafi da sunan mahaifinki. "Shi ma ya yi alfaharin ya haife ki, in shahara kikai, in ɗaukaka kikai, in daraja kikai, ya zamana akwai sunan mahaifinki a ciki".

Ya ce ko da yake a Musulunce, mace ba ta canza sunan mahaifi da na mijinta, amma tana iya ƙarawa da sunan mijin ko dangin miji. Amma ba za a cire sunan mahaifi ba. "Musulunci ya hana."

Shehin malamin ya ce miji ba shi da hujjar tursasa wa matar da yake aure a kan ta cire sunan mahaifinta, ta sanya nasa a gaban sunanta.

"Kenan, mahaifinta ba shi da daraja da ƙimar da za ta ci gaba da amsa sunansa bayan ya tsugunna ya haife ta, saboda kawai za a aure ta. A kan me?"

'A dokokin ƙasa, ba shi da tushe'

Shi ma wani masanin dokoki a Najeriya, Dr Sulaiman Usman Santuraki ya ce tsarin mulkin ƙasar bai yi wani tanadi game da matsalolin rayuwar aure kamar wannan ba.

A cewarsa, batun ba sharaɗi ne na doka ba a Najeriya.

Ya ce al'adar mai yiwuwa ta samo asali ne kawai daga ala'adun Turawan Yamma, kuma abin ya samu karɓuwa sosai a wajen mutane da dama.

Dr. Sulaiman Santuraki ya ce al'adar ta samu wurin zama ne musamman saboda takardun tafiye-tafiye kamar na fasfo, waɗanda a lokuta da yawa ake samun cikas idan ma'aurata sun zo tafiya wata ƙasa, amma kuma sunan danginsu bai zo ɗaya ba.

Masanin ya ce a ganinsa bai kamata batun sunan ya zama wata hujja da za ta kawo matsala a tsakanin ma'aurata ba, sai dai fa idan akwai rashin fashimta.