BBC Hausa of Tuesday, 7 February 2023

Source: BBC

Talauci ne ke ingiza ƴan Afirka shiga ƙungiyoyin ta'addanci - MDD

Hoton alama Hoton alama

Wani sabon rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa rashin aikin yi shi ne babban abin da ke sa mutane shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a kasashen da ke kudu da hamadar Sahara da ke Afirka, ba addini ba.

Rahoton wanda hukumar shirin samar da ci-gaba ta Majalisar ta fitar, ya gudanar da bincike a kan dubban mutane a kasashe takwas na Afirka da suka hada da Mali da Najeriya da kuma Somalia.

Daga cikin wadanda masu binciken suka tattauna da su kan dalilinsu na shiga kungiyoyin masu ikirarin jihadi, kashi 17 cikin dari ne kawai suka ce akida ce ta addini ta sanya su, yayin da kashi 40 cikin dari suka danganta shigar tasu da fatara da talauci.

Rahoton ya kuma gano cewa ilimi yana da muhimmiyar rawar da zai taka a irin wannan yanayi wajen hana masu shiga kungiyoyin afkawa cikinsu.

Binciken ya nuna cewa samun karin shekara daya kacal ta ilimi na iya matukar rage yuwuwar mutum shiga irin wadannan kungiyoyi.

Alkaluma sun nuna cewa a 2021, kusan rabin mace-macen da aka samu a duniya masu nasaba da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ikirarin jihadi sun auku ne a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Shugabar ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kan matsalar miyagun kwayoyi da aikata miyagun laifuka, Ghada Waly ta ce a shekarar ta 2021 kusan rabin mutane 3,500 da suka hallaka a sanadiyyar ta’addanci daga wannan bangare na Afirka suke.

Hukumar ta ce binciken da aka gudanar a lokacin ya nuna cewa yawancin yankin Sahel musamman ya zama wata babbar matattara ta kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Ms Waly ta ce yana da kyau a san dangantakar hakan da kuma kwararar kungiyoyin zuwa wannan yanki da kuma aikata miyagun laifuka.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ma’adanan da suka hada da zinare da azurfa da daiman da sauran duwatsu masu daraja na samar da makudan kudade ga kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi inda ake safarar wadannan albarkatu zuwa kasuwannin duniya.

Wannan kuma ba karamin amfani ba ne ga kungiyoyin wadanda ke samun iko da yankunan, inda ta haka kuma suke kara samun mabiya wadanda fatara da talaucisuka yi musu katutu.

Hakan ke kara sa wadannan kungiyoyi samun mabiya galibi matasa marassa aikin yi, wanda hakan ke sa kungiyoyin samun karfi da iko a yankin.

Wata hanyar da ake ganin kungiyoyin na samun kudade a binciken da aka yi ita ce, safarar namun daji, shugabar ta ce haramtaccen kasuwancin hauren giwa kadai yana samara da dala miliyan 400 a duk shekara

Afrika wadda ke da yawan jama'a sama da mutum biliyan daya da miliyan dari uku, kusan miliyan 500 daga cikinsu na rayuwa ne cikin tsananin fatara da talauci a shekara ta 2021, kamar yadda shugabar hukumar ta ce.

Waly ta ce wannan aiki da ake yi na hakar ma'adanai ta haramtacciyar hanya da da kuma haramtacciyar safarar namun daji na kwashe wa Afirka dimbin dukiya.

Wanda hakan kuma na hana miliyoyin mutanenta arzikin da za su rayu a kai, har ya haifar da karin rashin kwanciyar hankali da rikice-rikice, tare da shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a matsayin wata mafaka ga dimbin wadanda ba su da aikin yi a nahiyar ta Afirka.

Matsalar sauyin yanayi da kuma annobar Korona kari da wannan hali da yankin na hamadar Sahara ya samu kansa a ciki na dankwafe shi.

Wannan ne kuma zai kara jefa wannan yanki na Afirka cikin hali na rashin ci-gaba.