BBC Hausa of Wednesday, 21 June 2023

Source: BBC

Tasirin ɓangaranci a naɗin hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A ranar Litinin ne, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaro da babban sufeton 'yan sanda, bayan ya sallami tsoffin jagororin tsaron ƙasar daga aiki a wani mataki na yi wa fannin tsaro garambawul.

Naɗa sabbin hafsoshin tsaro a Najeriya, ba sabon mataki ba ne a wajen sabbin shugabannin ƙasa da suka kari ragamar mulki a Afirka.

Bayan shigarsu ofis, suna ƙoƙarin naɗa sabbin ministocin da za su taya su tafiyar da gwamnati.

Naɗin sabbin shugabannin tsaron a baya-bayan nan ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda wasu ke ganin Bola Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ne domin ci gaban ƙasa, a ɗaya gefen kuma wasu na ganin shugaban ya naɗa mutanen da zai ji daɗin aiki da su ne kawai.

Batun ɓangaranci da yankin da sabbin manyan hafsoshin tsaron suka fito, na cikin abubuwan da suka fi jan hankali, musamman a shafukan sada zumunta.

Mutane da dama sun yi ta kwatanta naɗe-naɗen sabon shugaban ƙasar, da na tsohon shugaban ƙasar Muhamadu Buhari.

Masu sharhi a shafukan sada zumunta sun yaba da naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron, inda suke ganin matakin ya dace saboda ya yi ƙoƙari wajen tabbatar da wakilcin duk manyan ɓangarorin ƙasar.

Hakan dai na nuna an yi aiki da tsarin tabbatar da rabon muƙaman gwamnatin tarayya bisa tanadin tsarin mulkin ƙasar.

Osikhena Dirisu, wani mai gabatar da shirye-shirye a radiyo, ya kuma wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Na ji daɗin kasancewar manyan hafsoshin tsaron suna wakiltar duka ɓangarorin ƙasar.

Shi ma wani mai amfani da shafin na Tiwtter mai suna @el_bonga ya rubuta cewa:

Sai dai, Nnedi Ogaziechi, mai sharhi kan harkokin siyasa, kuma marubuciya ta bayyana wakilcin ɓangarorin Najeriya wajen naɗa sabbin hafsoshin tsaron a matsayin “wani abu maras ƙayatarwa”.

''Ban damu da wanda Tinubu ya naɗa ba. Abin da nake so shi ne a samu jajirtattun da za su taimaki ƙasa''.

“A ganina wannan batun bai kamata ba, ba haka ya kamata ba'' ta ƙara cewa.

Ta ce a ganinta abin da ya kamata a yi la'akari da shi wajen naɗa manyan hafsohin tsaron Najeriya shi ne ''ƙwarewa'' da ''cancanta''.

Da yake zantawa da BBC, Kabir Adamu, wani masanin harkokin tsaro a Najeriya ya yaba da naɗin sabbin hafsoshin tsaron, musamman yadda aka samu wakilcin duka ɓangarori ƙasar.

Ya kuma ce duk da yake, Tinubu bai gama naɗe-naɗensa a ɓangaren tsaro ba, amma ''wani abin takaici game da naɗe-naɗen da gwamnatin Buhari da ta Tinubu suka gaza yi shi ne rashin sanya mata da matasa a muƙaman tsaron ƙasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasta cewa yawan al'ummar Najeriya ya zarce miliyan 206 a shekarar 2021, inda mata ke da kashi 49.95%, yayin da kashi 60% suka kasance matasa 'yan shekara 25 zuwa ƙasa.

Samun daidaiton wakilcin ɓangarorin ƙasar a muƙaman manyan hafsoshin tsaro, shi ne abin da ya mamaye zukatan al'ummar Najeriya a tsawon wa'adin gwamnatin Buhari.

Batun samun daidaito a duka ɓangarorin ƙasar ya samo asali ne tun bayan samun 'yancin kan Najeriya.

To amma daidai a riƙa la'akari da yankuna wajen naɗa hafsoshin tsaron?

Najeriya ƙasa ce mai ƙabilu da yawa, inda take da aƙalla ƙabila 500, ciki har da manyan ƙabilun ƙasar uku, wato Igbo a yankin kudu maso gabas sai Yarabawa daga yankin kudu maso yamma, akwai kuma Hausa/Fulani a yankin arewacin ƙasar.

A baya, duka manyan ƙabilun suna zaune a matsayin al'ummomi masu cin gashin kansu, kafin Turawan mulkin mallaka na Birtaniya su haɗe su zuwa dunƙulalliyar ƙasa ɗaya, mai gwamnati tarayya a Abuja, da gwamnoni a jiha 36 na ƙasar.

An kwashe shekaru masu yawa ana ce-ce-ku-ce a kan riƙe madafun iko a ƙasar, inda wasu yankunan ke ganin cewa ba a yi musu adalci, idan aka zo batun rabon muƙamai.

Lamarin da a lokuta da dama ke haddasa tashin hankali da zanga-zanga har ma da rikice-rikice, kai ya ma taɓa jefa ƙasar a yaƙin basasa.

Bayan ƙarewar yaƙin basasar ne, aka ɓullo da batun tabbatar da daidaito a aikin gwamnati cikin tsarin mulkin ƙasar na 1979.

Manufar haka, ita ce samun wakilcin ɓangarori da addinai da ƙabilun ƙasar a kowanne fanni.

Ƙaruwar masu kiraye-kirayen ɓallewa

A ƙarƙashin mulkin Muhammadu Buhari, an yi ta samun ƙaruwar masu kiraye-kirayen ɓallewa a sassan ƙasar, inda 'yan a-waren IPOB a yankin kudu maso gabashin Najeriya suka riƙa neman ɓallewa domin kafa ƙasarsu.

Haka kuma a yankin kudu maso yammacin ƙasar, Yarabawa sun yi ta kiraye-kirayen ɓallewa domin kafa tasu ƙasar.

Kabiru Adamu ya ce ''ɗaya daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar tsaro a Najeriya shi ne damuwar da ke cikin zukatan mutane''.

Ya nunar da batutuwan da suka shafi damuwar da mutane ke da ita da ƙaruwar masu rajin kare al'ummomin yankunansu, waɗanda akasari ke ganin ana mayar da su saniyar ware, kuma haƙiƙa a wasu lokutan saniyar waren ake mayar da su.

Ya ce wannan damuwar da kuma kiraye-kirayen ɓallewar yankuna, su ne manyan rashe-rashen adalcin da masu iko ke yi.

Da yawa na zargin cewa, an samu ƙaruwar kiraye-kirayen masu fafutukar neman ɓallewa a lokacin mulkin Buhari ne saboda zargin sa da nuna ɓangaranci wajen naɗe-naɗen muƙamai.

A ƙarƙashin sabuwar gwamnatin Tinubu, 'yan ƙasar na cike da fatan samun sauyi musamman a fannin tsaro.

A baya-bayan nan ana samun ƙarin kai hare-hare da kashe-kashen rayuka tare da lalata dukiyoyi a sassan ƙasar.

Mafi yawan hare-haren 'yan Boko Haram ne da 'yan fashin daji ke kai wa, musamman ma ta hanyar sace mutane don neman kuɗin fansa.

Majalisar Dinki Duniya ta ce ƙungiyar Boko Haram ta kashe mutane aƙalla 350,000 a 2020, tare da raba miliyoyin 'yan ƙasar da muhallansu, musamman a yankin arewa.

Cibiyar tattara alƙaluma kan rikice-rikice ta ACLED ta ce fiye da ɗalibai 1,000 aka yi garkuwa da su a tsakanin watan Disamban 2020 zuwa Yunin 2021, inda aka biya miliyoyin kuɗi kafin sakin da yawa a cikinsu.

Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consultancy ya ce 'yan ƙasar 78,000 ne aka kashe a cikin shekara 10 a sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa sabbin hafsoshin tsaron Najeriyar za su yi aiki tuƙuru wajen rage yawan kashe-kashen da ake fama da su.

Baya ga jan aikin da ke gaban sabbin hafsoshin sojin, 'yan Najeriya da dama na buƙatar samun shugabancin majalisar tsaron ƙasar mai ƙarfi wadda shugaban ƙasar zai jagoranta.

A ƙarƙashin gwamnatin Buhari, an yi ta sukar majalisar tsaron musamman a kan rashin sauya manyan hafsoshi, a lokutan da aka samu taɓarɓarewar harkokin tsaro

Kabiru Adamu ya ce ''an samu matsalar rashin yi wa mutane bayani game da abubuwan da ke faruwa a gwamnatin Buhari, abubuwa da dama sun faru kuma babu wanda zai iya yi maka bayanin faruwarsu''.

''Duk mutumin da ya kasa gudanar da aikin da aka ɗora masa, kawai a sauke shi'', in ji masanin.

Wasu abubuwan da suka faru a shekara ukun da ta gabata ƙarƙashin mulkin Buhari, sun haɗar da harin da 'yan bindiga suka kai wa ginin kwalejin nazarin harkokin tsaro da ke Kaduna (NDA), lamarin da ya janyo mutuwar manyan sojoji guda biyu tare da sace ɗaya.

Haka kuma an samu wani mummunan hari a kan wata coci a Owo da ke jihar Ondo,

Sannan an kai farmaki gidajen yari a faɗin ƙasar ciki har da harin 'yan Boko Haram a kan gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda suka kuɓutar da fursunoni aƙalla 400, mafi yawa mambobin ƙungiyar ne.

Ga kuma batun kai wa jirgin ƙasan fasinjan Abuja zuwa Kaduna hari, inda aka kashe wasu fasinjoji tare da yin garkuwa da wasu gommai.

A lokacin jawabin na kama aiki, sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi alƙawarin kawo 'sauyi' musamman a fannin tsaron ƙasar.