BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Tawagar Ingila ta mata ta jingine batun ladan wasa zuwa bayan kofin duniya

Yan wasan Ingila Yan wasan Ingila

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Ingila ta dakatar da tattaunawa da hukumar kwallon kafar kan batun ladan wasa, inji kyaftin Millie Bright.

Ta sanar ranar Talata cewar tawagar ta yi takaici da ba a kamo bakin zare ba kawo yanzu, inda ake jan kafa.

'Yan wasan na fatan kawo takaddama da take yi da hukumar kwwallon kafar Ingila kan ladan wasa, bayan da Fifa ta sanar da kudin da za ta biya ga duk kasar da ta lashe kofin duniya.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta ce za ta biya ladan da zai fara daga dalar Amurka 30,000 zuwa 270,000 ga kowacce 'yar wasa idan tawagarta ta lashe kofin duniya.

Hukumar kwallon kafar Ingila ba ta yi niyyar bai wa 'yan wasanta lada ba daga kudin da za ta samu daga Fifa idan kasar ta taka rawar gani.

Tawagar Ingila za ta fara wasan farko a gasar kofin duniya da Haiti a gasar da Australia da New Zealand za su yi hadakar karbar bakunci daga 20 ga watan Yuli.

'Yan wasan Ingila sun ce sun dakatar da batun tattaunawa da hukumar kwallon kafar kasar har sai bayan kammala gasar kofin duniyar.