You are here: HomeAfricaBBC2023 09 06Article 1839434

BBC Hausa of Wednesday, 6 September 2023

Source: BBC

Ten Hag na da muhimmaci a tarihin sana'ar ƙwallona - Amrabat

Kocin Manchester United Ten Hag da Sofyan Amrabat Kocin Manchester United Ten Hag da Sofyan Amrabat

Sabon ɗan ƙwallon da Manchester United ta ɗauka a bana, Sofyan Amrabat ya bayyana Erik ten Hag a matsayin wani mutum mai muhimmanci a tarihin taka leadarsa.

Ɗan wasan mai shekara 27, ya koma Old Trafford daga Fiorentina, domin buga wasannin aro zuwa ƙarshen kakar bana a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar saye da sayar da 'yan ƙwallo ta bana.

Ya taka leda a makarantar Utreacht, wadda ya yi wa babbar ƙungiyar wasa 50 a ƙarƙashin Ten Hag tsakanin 2015 zuwa 2017.

''Ya taka rawar gani a fannin tarihin taka ledar da na yi, kamar yadda ya sanar a shafin intanet na United.

''Ina ɗan shekara 19, amma ya ba ni damar buga wasa tare da manyan 'yan ƙwallon ƙungiyar ta Utrecht.

"Abu ne mai kyau domin yana sa ɗan kwallon ya buga wasa da zai kai shi kan ganiyar da zai ciyar da ƙungiya gaba.''

Amrabat, ɗaya daga fitattun 'yan wwasan tsakiya da suka taka rawar gani a Morocco yayin gasar cin kofin duniya a Qatar 2022, ya koma United don ƙara ƙarfin ƙungiyar.

United ta biya Fiorentina fam miliyan 8, da 600,000 da yarjejeniyar sayen ɗan ƙwallon a kan sama da fam miliyan 17 da ƙarin tsarabe-tsarabe na sama da fam miliyan 4.

United tana ta 11 a teburin Premier League da maki shida, bayan cin Wolves da Nottingham Forest, Tottenham da Arsenal suka doke ta.