Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar - CBN Godwin Emefiele daga mukaminsa.
Sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar kasar ta ce an dakatar da gwamnan CBN ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin kudi a kasar.