Donald Trump ya musanta tuhumar da ake yi masa ta karkatar da wasu muhimman bayanai a wata kotun tarayya da ke Miami a jihar Florida.
Mista Trump shi ne shugaban Amurka na farko - na yanzu ko na baya - da gwamnatin tarayya ta tuhume shi.
An rangwanta masa batun a batun daukan hoton masu laifi, amma ana sa ran za a dauki hoton yatsunsa kuma zai bayar da samfurin DNA.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Mista Trump ya gurfana a gaban kotu a bana, amma shari'ar ta ranar Talata ta fi tsanani.
A cikin kotu lauyan Mista Trump ya musanata tuhumar da ake yi masa kan aikata laifuka 37 da suka hada da rike wasu takardu ba bisa ka'ida ba da kuma kawo cikas ga kokarin da gwamnati ke yi na dawo da su.
"Tabbas mun musanta duk tuhume-tuhumen da ake yi mana," lauya, Todd Blanche, ya shaida wa alkalin.
Tsohon shugaban ya bayyana a gaban kotu, yana zaune sanye da riga mai duhu da hanayensa a nade.
Wanda ake zargi tare da Mista Trump, Walt Nauta - wanda mutum ne na kusa da shi kuma ake tuhuma da aikata laifuka shida a cikin shari'ar - yana zaune a teburi daya da tsohon shugaban kuma shi ma ya musanta aikata laifin.
An bai wa tsohon shugaban mai shekaru 76 damar ficewa daga kotu ba tare da takura ba, kamar yadda CNN ta ruwaito, bayan da masu gabatar da kara suka shaida wa alkalin kotun majistare Jonathan Goodman cewa ba a tunanin cewa zai iya tserewa.
Wasu motoci ne suka kai Mista Trump - wanda ke kan gaba a zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican a 2024.
Yayin da Trump ke kan hanyar zuwa kotu an wallafa sakonni da dama a dandalin sada zumunta mai suna Truth Social, ciki har da wanda aka wallafa cikin manyan haruffa da ke cewa: "Daya daga cikin ranaku mafi bakin ciki a tarihin kasarmu, mu al'umma ce da ke komawa baya!!!"
Alina Habba, wadda ita ce lauyar tsohon shugaban kasar, ta sake nanata ikirarin tsohon shugaban na cewa tuhumar na da alaka da siyasa yayin da take magana da manema labarai a wajen kotu.
Ta shaida wa manema labarai cewa "Muna kan wani mataki a tarihin al'ummarmu, matakin hukunta manyan abokan adawar siyasa irin abin da kuke gani a mulkin kama-karya kamar Cuba da Venezuela ne."
Ta kara da cewa "Abin da ake yi wa Shugaba Trump ya kamata ya tsoratar da dukkan 'yan kasar."
Maimakon daukan sa wani sabon hoto, wanda zai zama kamar cin fuska a gare shi, hukumar Marshals ta Amurka - wacce ke tsare kotunan tarayya - za ta yi amfani da tsohon hoton Mista Trump da aka dauka a baya, jami'ai a kotun sun yi wa manema labarai bayanin haka a safiyar Talata.
Ana sa ran cewa Mista Trump, wanda ya sha musanta aikata ba daidai ba, zai koma wurin shakatawa na wasan Golf a Bedminster, New Jersey.
Taron magoya bayan Trump da masu zanga-zanga sun taru a wajen kotun.
Hukumomin birnin sun shirya wa barkewar tarzoma, amma shugaban yankin Francis Suarez ya shaida wa manema labarai a yammacin ranar Talata cewa ba a samu wata matsala ta tsaro ba.