Shugaba Mahamat Idris Deby na Chad ya gudanar da tattaunawa mai zurfi da jagoran sojojin da suka yi juyin mulki cikin makon jiya a Nijar.
Ya je ƙasar ne a matsayin jakadan ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) don shawo kan shugabannin juyin mulkin Nijar su bar karagar iko, kuma su mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan kujera.
Wannan dai na ɗaya daga cikin buƙatun da ƙungiyar ECOWAS ta gabatar wa Nijar.
Deby a cikin wata sanarwa, ya kuma ce ya tattauna da hamɓararren shugaban Nijar wanda har yanzu ake ci gaba da tsare shi a Niamey.
Chadi maƙwabciyar Nijar ce daga gabas, kuma babbar abokiyar ƙawancenta ce. Su biyun duka suna cikin ƙungiyoyin soji da na farar hula, ciki har da Kungiyar raya Yankin Tafkin Chadi da Ƙungiyar Yaƙi da Kwararowar Hamada ta CILSS da kuma Rundunar Haɗin gwiwa mai Yaƙi da Boko Haram MNJTF.
A matsayinta na mai ƙarfin rundunar soji a Sahel, Chadi ta tallafa wa Nijar a lakutan da hare-haren masu iƙirarin jihadi suka sha kanta cikin shekarun baya-bayan nan.
Mahamat Deby dai na iya zama mutumin da shugabannin juyin mulkin Nijar za su fi ɗasawa da shi. Ba zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ba ne, jagoran mulkin soji ne da ya karɓi iko bayan mutuwar mahaifinsa. Kuma kasancewarta ba wakiliyar ECOWAS ba, sojojin Nijar suna iya fin amincewa da Chad a matsayin wadda za ta iya kwatanta adalci idan ta shiga tsakani a wannan dambarwa.
Babu masaniya ƙarara kan tasirin da ƙoƙarin Mahamat Deby zai iya, sai dai ga alama wa'adin kwana bakwai da barazanar ɗaukar matakin soji sun katse wa sabbin masu mulkin Nijar hankali.
Wani ƙwararre kan fannin tsaro a Najeriya, Dr Kabir Adamu ya ce matakin na ECOWAS ya zo musu da mamaki don kuwa ƙungiyar ba ta ɗauki irin wannan martani ba lokacin da sojoji suka ƙwaci mulki a ƙasashen Mali da Burkina Faso da Guinea.
Lamarin na daɗa zama mai wahala ga ƙungiyar bayan biyar daga cikin ƙasashe mambobinta 15 sun kuɓuce zuwa hannun sojoji a 'yan shekarun nan.
Idan tafiyar Deby ta yi nasara, sojojin Nijar suka amince su koma bariki, yankin na Afirka ta Yamma wanda mafi yawansa ke fama da rikicin masu iƙirarin jihadi tsawon shekaru, ya kauce wa sake tsunduma ƙarin wani tashin hankali.
Tunzuri dai ya ƙaru ranar Litinin a Niamey, bayan sojoji masu mulki sun zargi tsohuwar uwargijiyar ƙasarsu wato Faransa da yunƙurin "ƙaddamar da hare-hare don mayar da Bazoum kan mulki, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Sojoji masu mulkin Nijar sun kuma ce gwamnatin da suka hamɓarar ta bai wa Faransa izinin kai hare-hare a kan fadar shugaban ƙasa. Ma'aikatar harkokin wajen Faransa kamar yadda Reuters ya ruwaito, ba ta gaskata ko musanta samun izinin kai hari a Nijar ba.
Kabiru Adamu dai ya ce mai yiwuwa barazanar kai hari daga ECOWAS ta taso ne saboda shugabanta na yanzu wato shugaban Najeriya, Bola Tinubu, sabo ne a kan sha'anin mulki.
Mai yiwuwa zai so ya nuna irin ƙarfin mulkin da yake da shi ba tare da la'akari da matakan diflomasiyya ba.
Nan gaba ne, manyan hafsoshin tsaron ƙasashen ecowas za su yi wani taro don yanke shawara a kan matakan sojin da ake buƙatar ɗauka a kan hukumomin birnin Niamey. Kafin sannan da wuya a iya hasashen wuraren da dakarunsu za su kai wa hari, da girman hare-haren da za su ƙaddamar da kuma tsawon lokacin da za su ɗauka suna kai hare-haren kafin su iya cin ƙarfin masu mulkin na Nijar.
Tuni dai aka fara bayyana fargaba a kan sakamakon da irin wannan matakin sojoji zai iya haifarwa, idan ma ƙungiyar ecowas da gaske ta ƙaddamar da hare-haren a kan wata ƙasar yankin mai 'yancin cin gashin kanta.
Wasu ƙwararru kamar Dr Kabiru Adamu na ganin matakan diflomasiyya sai sun fi tasiri wajen shawo kan rikicin Nijar.
Ya ce sanya takunkuman da za su mayar da Niamey da sojoji masu mulki da magoya bayansu a ciki da wajen ƙasar saniyar ware, zai iya fin tasirin wajen ganin Nijar ta dawo cikin hayyacinta.