Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da Manchester United za ta yi da Chelsea ba a ranar Asabar. Dan wasan gaban Portugal ya bar Old TRafford kafin kallama wasan da ta yi da Tottenham ta samu nasara da ci 2-0 a ranar Laraba - saboda an barshi a benci ba a sa shi a wasan ba. "Sauran 'yan wasan kungiyar za su ci gaba da shirye-shirye na wasan gaba," kamar yadda wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana. United ta ce dan wasan mai shekara 37 na da matukar muhimmanci a tawagar, sai dai wannan mataki ne da ya shafi kwamitin ladabtarwa. Wasan da ba zai buga ba a Stamford Bridge na daya daga cikin manyan wasanni, yayin da United ke bin Chelsea da ke matsayi na hudu a baya da maki daya. Kafafen yada labarai da dama na rawaito cewa dan wasan yaki shiga canjin da za a sa shi a wasan Spurs saboda lokaci ya kure. A daidai minti na 89 Ronaldo ya fice daga filin wasan, yayin da United ta yi canji uku cikin biyar da take da shi. Kai tsaye ya shige dakin sauya kaya gabanin ficewa daga filin wasan baki daya. Bayan kammala wasan Erik ten Hag ya ce "zai ji da lamarin" a ranar Talata. A ranar Lahadi da United ta buga wasa da Newcastle, sai da Ronaldo ya nuna rashin jin dadinsa saboda an yi canjin shi.