BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Unai Emery ya lashe Euopa League na hudu a Tarihi

Villarael ta lashe Europa League a karon farko a tarihin su Villarael ta lashe Europa League a karon farko a tarihin su

Villarael ta lashe Europa League a karon farko a tarihi, bayan da ta doke Manchester United da ci 11-10 a bugun fenariti ranar Laraba a Poland.

Tun farko kungiyoyin sun tashi 1-1, inda Villareal ce ta fara cin kwallo ta hannun Gerard Moreno a minti na 29 da fara tamaula, kuma haka suka je hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Edison Cavani ya farke wa United kwallo da hakan wasa ya koma 1-1 kuma haka suka tashi.

Daga baya aka kara minti 30 da aka fara 15 sannan aka dan sha ruwa aka koma zagaye na biyu, amma karawar ba ci tsawon minti 120.

Hakan ne ya sa aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga da ake fara zabo 'yan wasa biyar-biyar daga kowacce kungiya.

Villareal ce ke fara buga fenariti, sannan United ta buga nata, kuma dukkan 'yan wasa biyar na Villareal sun ci kwallo.

Wadanda suka fara buga mata fenaritin sun hada da Gerard Moreno da Dani Raba da Paco Alcácer da Alberto Moreno da kuma Daniel Parejo.

Biyar din United da suka ci mata fenariti sun hada da Juan Mata da Alex Telles da Bruno Fernandes da Marcus Rashford da kuma Edinson Cavani.

An ci gaba da buga fenariti, inda Villareal ta yi nasara a nata ta hannun Moi Gómez da Raúl Albiol da Francis Coquelin da Mario Gaspar da kuma Pau Torres.

Itama United ta ci karin biyar da ta buiga ta hannun Fred da Daniel James da Luke Shaw da Axel Tuanzebe da kuma Victor Lindelof.

Daga baya ne Gerónimo Rulli ya ci wa Villareal na 10, shi kuwa golan United, David De Gea ya barar, aka tashi 11 da 10 a bugun fenariti.

Karawa da suka yi a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai:

2020/21

Europa League Laraba 26 ga watan Mayun 2021

  • Villarael 11-10 Manchester United


Sun tashi wasan 1-1 daga baya aka yi bugun fenariti

2008/2009

Champions League Talata 25 ga watan Nuwambar 2008

  • Villarreal 0 - 0 Manchester United
Champions League Laraba 17 ga watan Satumbar 2008

  • Manchester United 0 - 0 Villarreal
2005/2006

Champions League Talata 22 ga watan Nuwamba 2005

  • Manchester United 0 - 0 Villarreal
Champions League Laraba 14 ga watan Satumba 2005

  • Villarreal 0 - 0 Manchester United