Manchester United ta ki sallama tayin fam miliyan 20 da West Ham United ta yi, domin a sayar da Harry Maguire.
Koci, David Moyes na sa ran sayen Maguire, wanda yake da kudi a kasa, bayan da West Ham ta sayar da Declan Rice sama da fam miliyan 100 ga Arsenal a bana.
Maguire bai da makoma a kungiyar Old Trafford, bayan da Erik ten Hag ya karbe mukamin kyaftin din 'yan wasa a farkon watan nan.
Mai horar da United ya ce hakan zai sa dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 30 zai iya komawa kan ganiyarsa, domin an rage masa nauyin da yake kansa.
United na fatan saurara tayin da zai yi daidai da darajar dan kwallon, idan kuma Maguire ya amince yana son komawa wata kungiyar.
Mai tsaron bayan na karbar fam 200,000 a duk mako a Old Trafford, wanda ba dan kwallon West Ham da yake karbar albashi da yawa haka.
Ole Gunnar Solskjaer ya bai wa Maguire mukamin kyaftin a Janairun 2020, wata biyar tsakani da United ta saye shi daga Leicester City fam miliyan 80.
Maguire ya buga karawa 31 a wasa 62 da kungiyar ta fafata a kakar 2022-23 har da guda takwas a Premier League, yayin da Bruno Fernandes ke saka kyallen kyaftin idan dan Ingilar bai yi wasa ba.
Kwantiragin Maguire zai kare a Old Trafford a karshen kakar 2025.
United na amfani da masu tsaron baya da suka hada Raphael Varane da Lisandro Martinez a madadin Maguire, kuma idan wani daga ciki ya ji rauni sai ta yi amfani Victor Lindelof.
Haka kuma an yi ta sa Luke Shaw yana tsare baya daga tsakiya a United karkashinTen Hag.