Dan kwallon tawagar Italiya, Marco Verratti ya kammala komawa Al-Arabi ta Qatar daga Paris St-Germain kan fam miliyan 38,680.
Daya ne daga fitattun 'yan kwallon Turai da ya koma buga gasar tamaula ta Qatar a makon nan.
Ranar Juma'a dan wasan Aston Villa, Philippe Coutinho ya koma Al-Duhail, inda tsohon dan wasan Brazil zai buga wasannin aro zuwa ƙarshen kakar bana.
Verratti ya lashe Ligue 1 tara a PSG tun bayan da ya koma ƙungiyar a 2012, ya kuma taimaka wa Italiya ta ɗauki Euro 2020.
Verratti ya zama na baya-bayan nan daga Turai da ya koma gabas ta tsakiya da taka leda, bayan da yawa daga cikinsu suka koma buga gasar tamaula ta Saudi Arabia a bana.
A cikin watan Agusta, Neymar ya koma Al-Hilal kan fam miliyan 77.6 daga Paris St Germain.
Zai taka leda tare da Rafinha, tsohon dan wasan PSG da dan kwallon Brazil, Thiago, wanda ya bar Liverpool zuwa Al-Arabi, waɗanda suka taka leda a Paris tsakanin 2020 zuwa 2022.
Tun farko an alakanta Verratti da komawa Saudi Arabia da buga tamaula, amma ba ƙungiyar da ta taya ɗan wasan har ranar 7 ga watan Satumba da aka rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta kasar.