BBC Hausa of Wednesday, 15 November 2023

Source: BBC

Waɗanne ƙungiyoyi ne ke yajin aiki a Najeriya zuwa yanzu?

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Yajin aikin da manyan ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya ke yi, ya shiga kwana na biyu, yayin da ƙungiyoyin ma'aikata da dama suka ajiye aiki daga ranar Talata a sassan ƙasar.

Ƙungiyar ma'aikata ta Nigeria Labour Congress (NLC) da ta 'yan kasuwa Trade Union Congress (TUC) sun nemi ƙananan ƙungiyoyin da ke tare da su su shiga yajin aikin har sai gwamnati ta biya musu buƙatunsu.

"Sakamakon shawarar da kwamitin gudanarwa na NLC da TUC ya yanke, an umarci dukkan ma'aikata su jingine aiki daga ƙarfe 12:00 na dare a yau [Litinin] 13 ga watan Nuwamba," a cewar shugaban TUC Festus Osifo yayin wani taron manema labarai.

Babu tabbas game da tsawon lokacin da yajin aikin zai ɗauka, amma ana sa ran zai shafi muhimman ɓangarori kamar na lafiya, da sufuri, da ilimi na ƙasar da ta fi kowacce girman tattalin arziki a Afirka.

Ƙungiyoyi da dama ne suka umarci ma'aikatansu su zauna a gida don yin biyayya ga uwar ƙungiyarsu ta ƙwadago ta ƙasa.

Su wane ne suka shiga yajin aikin?

Yajin aikin na ci gaba ne duk da umarnin da kotun ɗa'ar ma'aikata ta bai wa 'yan kwadagon cewa kada su gudanar da shi.

Cikin manyan ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin akwai Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta malaman jami'a a Najeriya.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa "a matsayinu na mambobin NLC, muna umartar dukkan 'yan ƙungiyarmu su shiga yajin aiki don kare haƙƙin ma'aikata da kuma shugabannin ƙungiyar".

Jami'ar Bayero ta kano ta dakatar da jarabawar da ɗalibai ke yi ta zangon farko saboda yajin aikin.

Binciken da Sashen Pdgin na BBC ya gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin ɗalibai sun rubuta jarabawar a safiyar Talata kafin daga baya jami'ar ta fitar da sanarwar dakatarwar.

Ba ASUU ce kaɗai take yajin aikin ba a ɓangaren ilimi.

Ƙungiyoyin manyan ma'aikatan jami'a ta Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU), da ta malaman kwalejojin fasaha Academic Staff Union of Polytechnics (ASUP), da ta ma'aikatan kwalejojin Senior Staff Association of Nigeria Polytechnics (SSANIP), da ta ma'aikatan kwalejojin ilimi Colleges of Education Staff Union (COEASU) duk sun ba da umarnin dakatar da aiki.

Bayan ɓangaren ilimi, ƙungiyar likitoci da ma'aikatan lafiya ta umarci ma'aikatanta cikin wata sanarwa su fara yajin aikin na sai abi da hali ya yi.

Shi ma sashen sufuri da ya ƙunshi ma'aikatan sufurin jiragen ƙasa da na ruwa ya dakatar da ayyuka.

Sauran ɓangarrorin da lamarin ya shafa sun ƙunshi ƙungiyar ma'aikatan lantarki, da ma'aikatan harkokin kuɗi. Wata sanarwa daga ƙungiyar ma'aikatan banki da inshora ta ce ba za ta dawo aiki ba har sai ƙungiyar ƙwadago ta janye yajin aikin.

Saura ƙungiyoyin su ne ma'aikan kotuna ta JUSUN, ma'aikatan masaƙu, ƙungiyar malaman jinya da ungozoma, ƙungiyar ma'aikatan ƙananan hukumomi, ƙungiyar ma'aikatan gidan waya.

Sai dai duk da waɗannan umarni, babu tabbas ko duka 'ya'yan ƙungiyoyin za su yi biyayya 100 bisa 100.

Ko ma'aikata sun yi biyayya ga umarnin?

Sashen Pidgin na BBC ya bi diddigin yadda yajin aikin ke gudana tun daga ranar Talata.

A birnin Kano, aksarin mutane na ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda suka saba, in ban da ofisoshin gwamnati da suke kulle.

Haka nan, ɗaliban firamare da sakandare da dama da suka fita makarantu a safiyar Talata sai gida suka koma saboda babu malamai.

A sakatariyar Alausa da ke Ikeja a Legas, ayyuka ba su tsaya ba.

Wani ma'aikaci da ya nemi a ɓoye sunansa ya ce babu wanda ya umarce su da kada su je aiki. Amma ya ƙara da cewa komai zai iya sauyawa kafin Laraba.

Me ya sa 'yan ƙwadago ke yajin aikin?

Yajin aikin wani ɓangare ne na yunƙurin nema wa shugaban NLC Joe Ajaero haƙƙinsa, wanda ya yi zargin 'yan sanda sun ci mutuncinsa a jihar Imo ranar 1 ga watan Nuwamba.

Ajaero da sauran mambobin NLC sun ce sun je Imo ne da ke kudu maso gabashin ƙasar don taya ma'aikatan jihar gwagwarmayar neman albashinsu na wata 31 da suke bi da kuma ma'aikata 10,000 da aka ce na boge ne.

Sai dai a cewar shugabannin NLC, wasu 'yan daba da kuma jami'an tsaro sun kai wa Ajero hari tare da cin mutuncinsa, inda suka saka shi cikin motar 'yan sanda kuma suka tsare shi na wani lokaci.

Bayan faruwar lamarin ne kuma NLC da TUC suka yi barazanar tsunduma yajin aiki ranar 14 ga watan Nuwamba idan gwamnati ba ta biya buƙatunsu ba, ciki har da neman wani jami'in 'yan sanda ya yi ritaya.

"Mun buƙaci a cire kwamandan sashen da ya jagoranci 'yan sanda wajen cin zarafin daga muƙaminsa kuma a gurfanar da shi a kotu," in ji NLC.

"Haka nan, muna so a kama tare da gurfanar da mataimakain Gwamna Hope Uzodimma na musamman kan ayyuka na musamman, Chinasa Nwaneri, wanda ya jagoranci cin zalin."