BBC Hausa of Sunday, 17 December 2023

Source: BBC

Waiwaye: Dambarwar siyasar Rivers da Cire malaman jami'a daga IPPIS

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Wannan maƙala ce da ke zaƙulo muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Tinubu ya cire malaman jami'a daga tsarin albashi na IPPIS

A cikin makon da muke bankwana da shi ne majalisar zartarwa ta Najeriya ta cire malaman jami'a, da na kwalejojin ilimi da fasaha daga tsarin albashi na 'Integrated Personnel Payroll Information System' (IPPIS).

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya ba da umarnin yin hakan a zaman majalisar da ya jagoranta a ranar Laraba.

Ya ƙara da cewa hakan zai bai wa shugabannin cibiyoyin ilimin damar ɗaukar ma'aikata ba tare da sun nemi amincewar ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya ba.

Karanta cikakken labarin a nan

'Yan Najeriya na da 'yancin ɗaukar bidiyon 'yan sanda a bakin aiki'

A cikin makon ne kuma hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce 'yan ƙasar a da damar ɗaukar bidiyo da hotunan 'yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Alhamis.

Adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce 'yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.

Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon 'yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Ga cikakken labarin a nan

'Yan majalisar dokokin Rivers 27 sun fice daga PDP zuwa APC

A cikin makon ne kuma wasu 'yan majalisar dokokin jihar 27 suka bayyana ficewa daga jam'iyyar PDP tare da komawa jam'iyyar APC.

Wani al'amari da ya ja hankali mutane da dama a faɗin ƙasar cikin makon da ya gabatan.

Bayan bayyana matakin 'yan majalisar ne kuma, sai majalisar mai mabobi biyar ta ce ta kore su daga majalisar.

A ranar Laraba ne kuma gwamnan jihar ya bayar da umarnin ruguza ginin majalisar dokokin jihar, yana mai cewa an ɗauki matakin ne bisa dalilan rashin ingancin ginin.

Inda majalisar ta yi zamanta agidan gwamnati a ranar, har ma gwamnan jihar Siminalayi Fubara ya gabatar wa majalisar da kasafin kuɗin jihar don yin muhawara, inda nan take suka amince da shi.

A ranar Alhamis ne kuma gwamnan ya sanya hannu kan kasafin kuɗin.

Gwamnan Ondo Akeredolu ya fara hutun jinya

A cikin makon ne kuma gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya fara hutun jinya, kamar yadda mai magana da yawunsa, Richard Olatunde, ya bayyana.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Olatunde ya ce yayin da Akeredolu ke hutun, mataimakin gwamnan, Lucky Aiyedatiwa, zai karɓi ragamar lamurran jihar, a matsayin muƙaddashin gwamna.

Akeredolu, Babban Lauyan Najeriya (SAN), kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), ya sake lashe zaɓensa a matsayin gwamnan jihar a watan Oktoban 2020 kuma an rantsar da shi a karo na biyu a watan Fabrairun 2021.

Sai dai kuma, wa'adi na biyu na gwamnan, tun daga watan Janairun 2023, bai kasance cikin halin lafiya ba, domin sai da aka kai shi ƙasar waje neman magani a watan Yuni.

Ga cikakken labarin a nan

Kotun ƙoli ta ce dole Nnamdi Kanu ya fuskanci shari'a

A ranar Juma'a ne kuma kotun ƙolin Najeriya ta yi watsi da hukuncin wata kotun ɗaukaka ƙara ta ƙasar wadda ta ce madugun ƴan awaren Ipob, Nnamdi Kanu ba zai fuskanci shari'a ba kasancewar an kama shi ne ba bisa ƙa'ida ba.

Saboda haka nan alƙalan kotun suka ce za a ci gaba da yi wa Kanu shar'ia.

A yau ne kotun ta yanke wannan matsaya kan Nnamdi Kanu, wanda ke da mabiya a ciki da wajen Najeriya.

Shari'ar Nnamdi Kanu ta baya-bayan nan ta faro ne tun daga shekarar 2021, daga Babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Ga cikakken labarin a nan

Sakin ragowar ɗaliban Jami'ar Dutsin Ma

A ƙarshen mako ne kuma aka samu rahotannin sakin ragowar ɗaliban Jami'ar Tarayya ta Dutsin Ma, bayan shafe sama da wata biyu a hannun 'yan fashin daji.

Shugaban makarantar Farfesa Arma Ya'u Hamisu Bichi, ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin sakin sakin ɗaliban daga ɗaya daga cikin mahaifan ɗaliban da misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Ya ƙara da cewa an saki duka ɗaliban huɗu da suka rage a hannun 'yan bindigar.

A ranar Laraba 4 ga watan Oktoba ne, wasu 'yan bindiga suka auka gidan kwanan ɗaliban - dukkansu mata - da ke zaune a wajen jami'ar cikin unguwar Maryama Ajiri da tsakar dare.

Karanta cikakken labarin a nan