Wannan maƙala ce da ke yin duba kan muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
Ganawar Kwankwaso da Tinubu
A ƙarshen makon da ya gabata ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja.
Kwankwaso ya ce ya ji daɗi kan yadda Shugaban ƙasar yake nemansa don kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC bayan ganawa da shugaban ƙasar, jagoran na NNPP ya ce Tinubu ya yi masa tayin muƙami a gwamnatin, sai dai ya ce har yanzu ba su kai ga cimma matsaya ba.
Tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da dambarwa ke sake kamari tsakanin ɓangaren sabuwar gwamnatin Kano da kuma gwamnatin APC da ta shuɗe.
Karanta cikakken labarin a nan
Rufe majalisar dokokin Najeriya ta tara
Haka kuma a cikin makon da muke bankwana da shi ne ɗin ne kuma aka rufe majalisar dokokin Najeriya ta tara, bayan ta shafe shekara huɗu tana gudanar da aiki.
A Larabar 7 ga watan Yuni ne aka rufe majalisar wakilan Najeriya, a wani zama na ƙarshe da majalisar ta yi a harabar majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Yayin da aka rufe majalisar dattawan ƙasar ranar Asabar 10 ga watan Yuni.
Shekara huɗu ke nan majalisar ta yi tana zartar da dokoki da ƙudurori da batutuwa da shawarwari, baya ga bibiyar ayyukan ɓangaren zartarwa.
Majalisar ta yi aiki ne a wani lokaci mafi ƙalubale tun bayan komawar Najeriya kan tsarin dimokuraɗiyya a 1999, saboda annobar korona da karayar tattalin arziƙin da ƙasar ta fuskanta har sau biyu a zamaninta.
Karanta cikakken labarin a nan
Tinubu ya dakatar da gwamnan CBN Emefiele
A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin ƙasar - CBN Godwin Emefiele daga muƙaminsa.
Cikin wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar ta fitar ta ce an dakatar da gwamnan CBN ne domin a gudanar da bincike sannan kuma ya sauya fasalin harkokin kuɗi a ƙasar.
"Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban banki, Mr Godwin Emefiele, CFR daga ofis ba tare da ɓata lokaci ba," in ji sanarwar.
An umurci gwamnan CBN ɗin ya mika ragamar tafiyar da harkokin ofis ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa wanda zai kasance muƙadashin gwamna har sai an kammala bincike da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta bayyana cewa Emifiele na hannunta, domin gudanar da bincike, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter.
Samamen da jami'an tsaro suka kai gidan tsohon gwamnan Zamfara
Ƴan sanda sun kai samame a gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, wanda ba shi da nisa da gidan gwamnati a Gusau, babban birnin jihar.
A wata tattaunawa da BBC, tsohon daraktan yaɗa labaru na tsohon gwamnan, Yusuf Idris ya ce lamarin ya faru ne a yau Juma'a.
Wannan samame dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan gwamnan jihar Dauda Lawal Dare ya zargi Matawalle da wasu jami'an gwamnatinsa da yin sama da fadi da wasu kayayyakin gwamnatin jihar ciki har da matocin alfarma masu yawa.
Gwamnan ya kuma zargi Matawalle da yin awon gaba da motocin da ke gidan gwamnati kafin ya mika masa shugabancin jihar.
Sai dai a martanin da ya mayar tsohon gwamnan, Bello Muhammad Matawalle, ya ce sata aka je yi gidansa ba 'samame' ba.
Matawalle ya ce "sakarci ne" da "talauci" ya sa aka shiga gidan nasa, yana mai cewa an sace kayayyaki ciki har da hijabin matansa.
"Dukkan ɗakunan matana babu wanda ba a shiga ba, har da hijabi na mata aka kwashe. Hatta irin murhun nan na garwashi, duka an saka cikin mota an tafi da su," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin motocin da aka kwashe ya saye su ne daga Amurka tun kafin ya zama gwamna saboda da ma sana'arsa ce sayar da motoci.
Koken Ganduje ga Bola Tinubu kan Abba gida-gida
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya bayyana wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu halin da ake ciki kan maganar rushe-rushe a jihar Kano.
Ya kuma ce ya miƙa koke kan lamarin ga sifeta-janar na ƴan sandan ƙasar domin ganin an ɗauki mataki.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin ganawa da manema labaru bayan wata tattaunawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana abin da gwamnatin sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ke yi ta hanyar rushe gine-gine da abin da ya saɓa wa doka.
Majalisar Najeriya ta amince da dokar hukunta masu lalata da ɗalibai
A makon da muka fita ne Majalisar Wakilan Najeriya mai barin gado ta amince da ƙudirin dokar da zai haramta tare da hukunta duk malamin da aka samu da laifin cin zarafi ko lalata da ɗalibai a kwalejoji da jami'o'i a ƙasar.
Tun a shekarar 2020 Majalisar Dattawa ta amince da ƙudirin mai taken The Prevention, Prohibition and Redressal of Sexual Harassment in Tertiary Educational Institutions Bill amma ƙunshe da tanade-tanade daban.
Shugaban kwamatin Majalisar Dattawa kan harkokin shari'a, Sanata Opeyemi Bamidele, ya ce taron gamayyar 'yan majalisar ya haɗe kan tanade-tanaden biyu kafin ya gabatar da rahotonsa a zauren Majalisar ranar Laraba.
Cikin tanadin dokar, akwai matakan daƙile yunƙurin aikata lalata da kuma cin zarafi na jinsi a dukkan matakin karatu na gaba da firamare a Najeriya.
An fara sauraron ƙarar da APC ta shigar kan nasarar Abba Gida-gida
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta fara zaman share fagen shari'a, inda ta amince da bukatar INEC na aiwatar da wasu gyare-gyare a cikin ƙunshi martanin da ta shigar a gaban kotun.
Jam'iyyar APC reshen jihar Kano ce ta shigar da ƙara gaban kotun korafe-korafen zaɓen inda take ƙalubalantar nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a zaɓen ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Sauran mutanen da jam'iyyar APCn ta kai ƙara gaban kotun, har da hukumar zaɓe ta INEC da jam'iyyar NNPP.
A zaman kotun na yau an mayar da hankali ne, kan tsattsefe bayanai da takardun dukkan ɓangarorin da ke cikin shari'ar suka shigar gaban kotun
Kotu ta ce masu ƙalubalantar nasarar Tinubu su biya miliyan goma-goma
Babbar kotun tarayya da ke Abuja baban birnin Najeriya ta yi watsi da ƙasar da wasu mazauna birnin suka shigar a gabanta suna neman ta hana rantsar da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu.
Yayin da yake yanke hukuncin ranar Talata, alƙalin kotun, Mai shari'a Inyang Ekwo, ya umarci masu ƙarar da kowannensu ya biya naira miliyan 10 ga ministan shari'a kuma Atoni janar na ƙasar.
Masu ƙarar dai na iƙirarin cewa shugaban ƙasar Bola Tinubu bai samu samu kashi 25 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa a baban birnin tarayyar Abuja, dan haka suke ganin bai cancanci zama shugaban ƙasar ba.
Mai shari'a Ekwo ya ce masu karar ba su da 'yancin shigar da ƙarar a kotun, yana mai cewa a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ne kawai ya kamata a shigar da ƙasar, a maimakon babbar kotun tarayyar da ke Abuja.
Jihohi biyu sun rage kwanakin aikin gwamnati zuwa wuni uku a mako
Gwamnatin jihar Kwara a Najeriya ta amince da ɗaukar matakin wucin-gadi na rage adadin kwanakin aikin gwamnati a jihar domin rage wa ma'aikata raɗaɗin da janye tallafin man fetur zai haifar.
Wani saƙo da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Murtala Atoyebi, ya fitar kuma aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Facebook, ya ambato shugabar ma'aikata a jihar, Mrs Susan Modupe Oluwole na bayyana matakin,
Mrs Oluwole ta ce gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bayar da umarnin rage kwanakin aikin gwamnatin na wucin-gadi daga kwana biyar zuwa uku a kowane mako.
Shi ma gwamnan jihar Edo da ke kudu maso kudancin Najeriya Godwin Obaseki ya rage kwanakin aikin gwamnti a faɗin jihar daga wuni biyar zuwa uku a mako.
A wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talata ta ce matakin wani ɓanagare ne na rage wa ma'aikata raɗaɗi da matakin cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi zai haifar.
Karanta cikakken labarin a nan