Kamar ko wanne mako akan samun labarai ma su yawa da ke faruwa a faɗin duniya, haka abin yake a Najeriya.
Wannan maƙala ce da za ta yi waiwaye kan wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya daga ranar Lahadi 10 ga watan Satumba zuwa ranar Asabar 16 ga watan.
Bari mu fara da labarin da ya farantawa mutane da dama rai a Najeriya wanda ya shafi hulɗar diflomasiyya tsakaninta da UAE.
Dubai ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza
A ranar Litinin 11 ga watan Satumba ne Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta cire haramcin biza a kan 'yan Najeriya, kamar yadda fadar shugaban Najeriya ta bayyana.
Cikin wata sanarwa daga fadar shugaban ta ce United Arab Emirates (UAE) ta ɗauki matakin ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da takwaransa Mohamed bin Zayed Al Nahyan a yau Litinin a birnin Abu Dhabi.
"Kazalika, wannan yarjejeniyar na nufin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na Etihad da Emirates za su ci gaba da shiga da fita a Najeriya nan take," in ji sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar.
Ta ƙara da cewa yarjejeniyar ba ta ƙunshi biyan wani kuɗi ba a nan kusa tsakanin ƙasashen, yana mai nuni da miliyoyin dalolin da gwamnatin Najeriya ta riƙe wa kamfanonin jiragen na kuɗin tikiti.
Kusan shekara ɗaya ke nan da UAE ta dakatar da bai wa matafiya daga Najeriya biza, a rikicin diflomasiyyar da ya samo asali tun daga lokacin annobar korona.
Ɓarkewar wani rikicin siyasa tsakanin APC da PDP
Wata sabuwar gardama ta kaure tsakanin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya da kuma babbar jam'iyyar hamayya ta PDP bayan bayyanar wani kundi da ke kunshe da cikakken bayani a kan hukuncin da kotun sauraron korafin zaɓen shugaban kasa ta yanke wanda ke dauke da hatimin APC.
Jam'iyyar PDP na zargin cewa APC ce ta tanƙwara hukuncin, kuma wannan ne ya sa aka tsara yadda hukuncin zai kasance har ma ya fito da hatiminta.
Sai dai APC ta musanta, tana cewa ita ce ta buga hatiminta a jikin hukuncin bayan kotun ta bai wa kowa ce jam'iyya ainahin kwafin hukuncin ba tare da hatimin ba, don haka PDP zargi take yi irin na ganganci.
A dangane da lamarin ne PDP ta ce ta tsaya tsam ta yi nazarin kundin da ya ƙunshi cikakken bayanin hukuncin kotun.
Turjiyar ASUU kan shirin gwamnati na bai wa jami'o'i cin gashin-kai
Wata dambarwa da aka samu wa cikin wannan mako da ya gabata, ita ce turjiyar da Ƙungiyar Malaman jami'o'i ta ASUU ta nuna game da shirin gwamnati na bai wa jami'o'i cin gashin-kai.
Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya ASUU ta ce ba za ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayyar ƙasar na bai wa jami`o`i da manyan makarantu `yancin cin gashin-kai ba.
A wannan makon ne Ministan Ilimin ƙasar Farfesa Tahir Mamman, ya ce gwamnatin tarayyar na shirin fito da wasu sabbin hanyoyi ta yadda jami'o'i da manyan makarantun gwamnati za su dinga cin gashin kansu.
Ƙungiyar malaman jami'o'in ta ce irin cin gashin-kan da gwamnatin tarayyar ke tunani ba zai kasance alheri ba ga 'yan Najeriya.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban shiyyar Kano ta ƙungiyar, Farfesa Abdulkadir Muhammad, ya ce, abin da gwamnatin take son yi a yanzu ya saɓa da wanda suke hanƙoron a yi.
Najeriya za ta biya kamfanonin jiragen sama bashin da suke bin ta
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci babban bankin ƙasar ya dinga shirya zama da masu harkar sufurin jiragen sama duk bayan wata uku don duba hanyar biyan su bashin kuɗaɗen waje da suke bin ƙasar da ya kai fiye da dala miliyon ɗari shida.
A kwanan nan ne gwamnatin Najeriyar ta sasanta da ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, bayan ƙasashen biyu sun dakatar da harkar sufurin jiragen sama a tsakanin su.
Ministan sufurin Najeriya, Festus Keyamo ya ce "gwamnatin Najeriya ta damu sosai game da matsalolin da ake fuskanta a harkar sufuri, musamman matsalar ƙarancin kuɗaɗen waje, lamarin da ya janyo wa ƙasar wani abu mai kama da kantar biyan bashi, na kuɗaɗen wasu kamfanonin jirgin sama, na maƙuɗan kuɗaɗe da suka kai fiye da dala miliyan ɗari biyar.
Kuma a halin da ake ciki, gwamnatin kasar ta dukufa wajen magance wannan matsala da ke yin tarnaki ga harkar sufurin jiragen sama.
Tinubu ya gana da Ganduje da manyan hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu ya gana da wani ayari ƙarƙashin jagorancin shugaban jam'iyyar APC mai mulki, Abdullahi Uamar Ganduje a fadar gwamnatin Najeriya da ke Abuja.
Jaridar Punch ta ambata cewa ko da yake ba a bayyana manufar taron a bainar jama'a ba, amma dai ta fahimci cewa mahalarta sun gabatar da wata maƙala da ta ƙunshi muhimman shawarwari a kan hanyoyin da za a kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a faɗin ƙasar.
Jaridar ta ambato wata majiya na cewa taron wanda aka fara da tsakar ranar Alhamis ya buƙaci kasancewar manyan hafsoshin tsaron Najeriya saboda batun ya shafi al'amuran tsaron ƙasa.
Rikicin manoma da makiyaya a Najeriya, ya yi sanadin mutuwar ɗumbin 'yan ƙasar a kan abincin dabbobi wanda ke daɗa ƙaranci sakamakon gurgusowar hamada da ɗumamar yanayi da bunƙasar jama'a, ke faɗaɗa buƙatun ƙasar noma.
Ɗaukin dala biliyan 2.5 da MDD za ta kawo wa Najeriya don yaƙar yunwa
Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta alƙawarta samar da dala biliyan 2.5 domin taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na yaƙi da yunwa da wadata al'umma da abinci a ƙasar.
Daraktan hukumar a Najeriya, Mista David Stevesson, ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci ayarin jami'ansa don kai ziyara ga ministar jin ƙai da yaƙi da fatara, Dakta Betta Edu a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Ya ce "mun tattauna game da yaƙi da yunwa a Najeriya, da kuma ayyukan jin ƙai a kowacce ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar, sannan mun tattauna kan shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya .
Ya ce za a gudanar da shirin ne ta hanyar tallafa wa ƙananan hukumomi wajen sayen abinci domin rarraba wa mabuƙata, da kuma ba su tallafin kuɗi da na abincin kai tsaye.