BBC Hausa of Thursday, 14 September 2023

Source: BBC

Walker ya tsawaita zamansa a Man City

Kyle Walker Kyle Walker

Ɗan wasan baya na Ingila Kyle Walker ya saka hannu kan yarjejeniyar tsawaita zamansa a Manchester City ta shekara biyu.

Ɗan ƙwallon mai shekara 33 ya shiga shekarar ƙarshe ta kwantaraginsa, inda aka dinga alaƙanta shi da komawa Bayern Munich a ƙarshen kakar bara.

Walker ya lashe manyan kofuna 13 tsawon shekara shida da ya shafe a City kuma yarjejeniyar na nufin zai ci gaba da zama a ƙungiyar har 2026.

"Ina murna da saka hannu kan sabon kwantaragi. Makomata tana Manchester City kuma shi ne abin da ya fi dacewa da ni," a cewar Walker.

"Na ji daɗin shekaru shida da na kwashe a wannan kulob ɗin mai ban-ƙaye. Na samu ƙwararren koci, 'yan wasa masu kyau da kuma ma'aikata, ga kuma magoya baya mafiya kyau. Ina jin daɗi a kowane ɓangare," in ji shi.

Ɗan bayan mai buga ɓangaren dama ya koma City daga Tottenham kan fan miliyan 45 a Agustan 2017.

Walker ya buga wa City wasa 39 a dukkan gasanni a kakar da ta gabata amma ba a fara wasan ƙarshe da shi na Champions League ba, wanda suka buga da Inter Milan.