Bola Ahmed Tinubu, jajirtacce kuma fitaccen ɗan siyasa a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a ƙasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya.
Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya dade yana jan zarensa tun daga dawowar Najeriya kan mulkin dimokuradiyya a 1999 kuma da alama har yanzu zarensa bai tsinke ba sakamakon irin tasirin da yake da shi a siyasar Najeriya, musamman a kudu maso yamma.
Jama'a da dama na ganinTinubu a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon faɗa a ji da yake da shi a siyasar ƙasar Yarabawa da ma Najeriya.
Haka kuma ya kafa mutane da dama a Najeriya inda ya yi musu hanya suka samu muƙamai a tarayya da jihohi.
Yaruntar da karatu
An haifi Bola Ahmed Tinubu ne jihar Legas, cikin iyalin Tinubu da ya yi fice a jihar.
Ya halarci makarantar firamare ta St. John's da ke Aroloya da makarantar Children's Home a Ibadan, da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Daga nan sai ya wuce Kwalejin Richard Daley a Chicago da ke kasar Amurka, bayan samun gurbin yin karatu a Kwalejin.
Daga baya ya zarce zuwa Jami'ar jihar Chicago, a Illinois inda ya kammala ya kuma fito da Digiri a Harkokin Kasuwanci.
Tinubu ya kuma samu kyautar dalibi da yafi kwazo a Jami'ar da kuma shaidar karramawa a bangaren Akanta da Hada-Hadar kudi.
Da zuwansa Amurka a shekarar 1975 da taimakon mahaifiyarsa, matashin mai hazaka, da kuma ke da himmar ganin ya cimma burinsa.
Ya shiga yin ayyuka da za su kawo masa kudi kamar wanke tukwane a gidajen sayar da abinci da aikin gadi da kuma tuka motar-haya domin taimaka masa a bangaren karatunsa.
Baiwar da yake da ita ce ta sa ya shiga jerin dalibai masu hazaka na Kwalejin Richard Daley da kuma ta kai har ya kammala karatu a Jami'ar jihar Chicago a 1979 inda ya fito da digiri a bangaren Kasuwanci.
A shekararsa ta farko a Jami'ar Chicago, an karrama shi da mukamin malami mai taimakawa (tutor), domin taimakon wasu 'yan uwansa dalibai da ke kananan ajuzuwa.
Ƴan uwansa dalibai da dama sun yaba taimakonsa a bangaren karatunsu wanda har ta kai su ga samun sakamako mai kyau.
A tsawon shekaru da yayi a jami'a, Tinubu ya kasance dalibi mafi hazaka wanda ya yi ta samun kyautar dalibi mai kwazo da kuma shaidar karatu a bangaren Akanta da hada-hadar kudi, inda kuma ya kare digirinsa da sakamako mai daraja ta sama.
A matsayinsa na mai hankoron abubuwa masu kyau da za su zo, Bola ya tsaya tare da yin nasara a takarar shugaban daliban nazarin Akanta da Hada-hadar kudi na jami'ar jihar Chicago a shekarar sa ta karshe.
Zama Gwamnan Legas
Bayan samun nasarar zama gwamnan Jihar Legas a zabukan 1999, Tinubu ya jagoranci jihar har na tsawon shekara 8.
Bayan shigar sa ofis a watan Mayun 1999, Bola Tinubu ya jawo hazikan mutane a cikin gwamnatinsa, wanda tare suka tsara kyakkyawan shiri na shugabancin Jihar lagos.
Ajanda 10 da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai sun kunshi bangaren ilimi da lafiya da samar da ayyukan yi da rage talauci, da samar da wutar lantarki da ruwan sha da tsarin zirga-zirga mai kyau da kula da muhalli da doka-da-oda da samar da abinci da kuma farfado da bangaren aikin gwamnati.
Gwamnatin Tinubu, ta inganta tare da gyara tsarin mulki ta hanyar kirkiro da sabbin ma'aikatu irinsu ma'aikatar gidaje da ma'aikatar wasanni da ci gaban matasa da kuma ta harkokin mata da rage talauci.
A tsawon mulkinsa, Asiwaju Tinubu ya kawo hazikai da kuma kwararru a cikin gwamnatinsa a matsayin kwamishinoni da kuma masu ba shi shawara a bangarori da suka kware.
Ta hanyar tsare-tsare da aiwatarwa, gwamnatin Asiwaju Tinubu ta kara kasafin kudin Jihar Legas daga naira biliyan 14.200 a shekarar 1999 zuwa Naira biliyan 240.866 a shekarar 2007 domin Jihar ta samar da karin ababen more rayuwa ga al'ummarta.
Gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kiyaye rabon kasafin kudi na shekara da akalla kashi 60-40 bisa dari a kan kudin da ake kashewa na manyan ayyuka don tabbatar da an samar da ababen more rayuwa ga al'umma.
Iyali
Asiwaju Bola Tinubu yana da mata daya mai suna Oluremi Tinubu, wadda sanata ce mai wakiltar Jihar Legas ta tsakiya.
Ta kasance mai fafutikar kare hakkin jama'a da kuma mai ilimi da ake mutuntawa.
Tana kuma gudanar da ayyukan jin kai wadda aka karrama da lambar girmamawa ta kasa ta Officer of the Order of the Niger (OON).
Suna da 'ya'ya da kuma jikoki.