BBC Hausa of Monday, 21 August 2023

Source: BBC

Wanne hali Abdulrasheed Bawa ke ciki?

Abdurrasheed Bawa, tsohon shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa, tsohon shugaban EFCC

Masu fafutuka da lauyoyin kare 'yancin ɗan'adam a Najeriya na ci gaba da nuna damuwa a kan ci gaba da tsare dakataccen shugaban babbar hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC).

Suna kafa hujja da cewa ci gaba da tsare Abdurrasheed Bawa tsawon lokaci, ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, abu ne da ya saɓa wa tsarin mulki.

Tsawon kwana 67 kenan, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS take tsare da dakataccen shugaban na EFCC.

Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin ɗan'adam a Najeriya, Femi Falana, ya yi kira ga hukumar ta gaggauta sakin dakataccen shugaban na EFCC, ba tare da ɓata lokaci ba.

A cewarsa, umarnin tsare Abdurrasheed Bawa da wata kotun majistare ta bayar, ba ya kan ƙa'ida saboda babu wata kotun majistre da ke da ikon ba da umarnin tsare wanda ake zargi tsawon fiye da wata biyu, ba tare da an tuhume shi ba bisa tanadin tsarin mulki.

Babu wanda zai iya faɗar halin da dakataccen shugaban na EFCCn yake ciki tun bayan kama shi, a cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin fararen hula na arewacin Najeriya.

Ambasada Ibrahim Wayya, ya ce duk ƙoƙari da suka yi, na ji daga Bawa, ya ci tura.

Ya ce suna ta ƙoƙarin tuntuɓar waɗanda ya dace su san halin da yake ciki.

"Har yanzu babu wata kafa da aka samu da za ta iya ba ka bayanai a kan halin da yake ciki.

Mun yi ƙoƙarin samun waɗanda ke da kusanci da shi, don jin ko akwai wani bayani, amma su kansu suna jin tsoron magana, wataƙila suna fuskantar barazana," in ji Wayya.

Ya ce duk fafutukar da suke yi ma a yanzu ita ce ta sanin me yake faruwa da shi.

A wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi, Femi Falana ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa DSS, da daraktan shigar da ƙara na gwamnati da ma'aikatar sharia sun mutunta 'yancin Bawa da kuma na dakataccen gwamnan babban bankin ƙasar, Godwin Emefiele.

"Ya kamata a gurfanar da Bawa gaban kotu ko kuma a sake shi. Ci gaba da tsare shi ya saɓa wa doka," in ji Falana.

Yayin da jagoran masu fafutukar ke cewa: "An ƙi ba mu damar gani ko sanin halin da (Bawa) yake ciki. Muna so mu gan shi sannan mu tattauna da shi."

Ibrahim Wayya ya ce akwai hatsarin gaske a ce an tsare ɗan ƙasa, ba tare da an tuhume shi a kotu ba ko ma yunƙurin kai shi kotu, a kan zargin da ake yi masa.

Ya ce tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa hukumomi ba su da ikon tsare wani ɗan ƙasa fiye da tsawon sa'a 48.

"Mun zauna a matakin ƙungiya kuma mun tattauna domin sanin mataki na gaba da za mu ɗauka,".

Me ake zargin Bawa da shi?

A ranar 14 ga watan Yuni ne, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da dakatar da shugaban hukumar na EFCC AbdulRasheed Bawa.

Wata sanarwa da aka fitar lokacin, ta ce Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin ne domin bayar da damar gudanar da bincike a kan wasu manyan zarge-zarge da ke kan Bawa.

Sai dai tsawon fiye da wata biyu ana tsare da Bawa, har yanzu gwamnati ba ta yi iya gabatar da wata tuhuma a kansa ba.

Masu lura da al'amura na ganin Abdurrasheed Bawa da dakataccen gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun ƙara shiga takun-saƙa da sabuwar gwamnatin Tinubu ne, a wani ɓangare saboda rawar da suka taka a harkar canza takardun naira, ana gab da shiga zaɓukan 2023.

Gwamnatin wancan lokaci ta ce ta ɓullo da matakin ne saboda ɗumbin kuɗin da ke hannun jama'a amma ba sa komawa cikin bankuna, da hana 'yan siyasa amfani da kuɗi don tafka maguɗin zaɓe.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin, ya bayyana damuwa a kan matakin canza takardun kuɗin na gwamnatin Buhari, wanda ya ce zai ƙara matsi da ƙunci ga al'ummar Najeriya.

EFCC a ƙarƙashin Abdulrasheed Bawa ta riƙa yin dirar mikiya a kan mutanen da aka samu suna ɓoye takardun kuɗi a lokacin da aka taƙaita yin haka, cikinsu kuma har da 'yan siyasa.

Haka zalika, dakataccen shugaban na EFCC ya sanya ƙafar wando ɗaya da wasu 'yan siyasa, waɗanda ya bayyana nemansu a hukumar, saboda binciken wata badaƙalar kuɗi da ake yi musu.

Me iyalan Abdurrasheed Bawa ke cewa?

"Duk wata hanya da za a bi, don ganin iyalansa sun san halin da ake ciki abin ya ci tura," in ji Ibrahim Wayya.

Ya ce suna tuntuɓar dangin Abdurrasheed Bawa don sanin halin da iyalansa ke ciki.

Ya ce duk da yake, babu wani firgici da suka nuna game da rashin sanin halin da Bawa yake ciki, amma sun kasa ji daga gare shi tsawon lokaci.

"Mahaifinsa ma yana cikin ƙoshin lafiya, yana kuma gudanar da harkokinsa na yau da kullum. Mahaifinsa ya fawwala komai ga Allah".

Ya ce dole su bi hanyoyin da suka dace don tabbatar da masa ƴanci a matsayinsa na ɗan Najeriya.

Kamata ya yi hukumar DSS, in ji Ibrahim Wayya, ta fito ta faɗa wa ƴan Najeriya tuhumar da suke yi wa Abdurrasheed Bawa da kuma ko suna shirin kai shi kotu.

"Shi ma Abdulrasheed Bawa ya kamata, hukumomi su fito su bayyana mana tuhumar da suke yi masa kamar yadda muka ga an yi wa Emefiele a kwanan nan.

Yanzu ƴan Najeriya sun san zargin da shi ake yi masa saɓanin Bawa," in ji ɗan fafutukar.

"Abin da muke so gwamnati ta sani, shi ne Abdulrasheed Bawa ya hidimta wa ƙasa, kuma duk laifin da ake zargin sa da aikatawa, bai kai girman da za a ci gaba da tsare shi babu shari'a ba".

Ya ce a ganinsu laifin da ake zargin shugaban na EFCC bai kai a hana shi beli ba.