BBC Hausa of Friday, 1 September 2023

Source: BBC

Wasu abubuwan da ƙila ba ku sani ba game da ƙasar Gabon

Pierre-Emerick Aubameyang Pierre-Emerick Aubameyang

Kwanaki kaɗan bayan da sojoji suka hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo, mutane da dama na kwaɗayin sanin bayanai game da ƙasar.

Ga waɗanda ba su da cikakkiyar masaniya kan lamurran ƙasar, mun kawo muku taƙaitattun bayanai kan ƙasar, mai ɗinbin arziƙi, wadda Faransa ta yi wa mulkin mallaka, wadda kuma iyalin Bongo suka daɗe suna mulka tun bayan samun ƴancin kai.

"Daular tsakiyar Afirka"

Ana mata laƙabi da "Ƙaramar daular tsakiyar Afirka" saboda ɗinbin arziƙin man fetur da aka gano a ƙasar cikin shekarun 1970.

Kasancewar al'ummarta ba su da yawa, wannan ya sa an samu mutanen masu matsakaicin ƙarfi da dama a ƙasar - kuma man fetur ne ke samar wa ƙasar kashi 60 cikin 100 na kuɗin shiga.

Kashi 90 cikin ɗari na ƙasar ƙungurmin daji ne

Ƙungurmin daji ne ya mamaye kimanin kashi 90 cikin ɗari na faɗin ƙasar. Dazukan na zuƙe sanadarin carbon da ƙasar ke fitarwa.

Waɗannan dazuka na samar da wurin zama ga giwaye da gwaggon biri da sauran namun daji.

Bature ya taɓa zama minista a ƙasar

Lee White, ɗan asalin ƙasar Birtaniya ya zama ministan kula da dazuka da muhalli da kuma sauyin yanayi na ƙasar a 2019.

Wannan ne ya sanya ƙasar ta zamo ƙasar Afirka ta farko da ta samu kuɗaɗe daga hukumomin duniya domin ta rage yawan sanadarin carbon a duniya ta hanyar kare dazukanta.

Pierre-Emerick Aubameyang

Shahararren tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang, wanda yanzu yake wasa a Marseille, shi ne wanda ya fi ci wa ƙasar ƙwallo a tarihi.

Duk da cewa an haife shi ne a Faransa, mahaifinsa ɗan asalin ƙasar Gabon ne kuma tsohon ɗan wasa da ya buga wa ƙasar.

A lokacin da yake matashi, burin hamɓararren shugaba Ali Bongo shi ne ya zama mawaƙin pop.

Ya saki wasu jerin waƙoƙi a shekarar 1978, a lokacin an fi sanin sa da suna Aalin Bongo.