Kasashe da dama na duniya na ci gaba da fama da tsananin zafi mai hadarin gaske, inda hukumomi ke ba jama’a shawarwari kan irin matakan da za su dauka na kare kai da sauran masu rauni daga illar yanayin.
A wasu kasashen ma ta kai ga ana kwashe mutane daga yankunansu saboda illar gobarar daji, wadda yanayin zafin ke haddasawa.
Tuni kasashe da dama musamman wadanda suke bangaren arewacin duniya suke fama da wannan matsala ta tsananin zafi da kusan ba a taba ganin irinta ba a baya.
Kasashen su ne na nahiyar Amurka ta Arewa da Turai da yawancin kasashen Asiya da wasu kasashen arewa maso kudancin Latin Amurka da kuma Arewacin Afirka.
Kasashen da ke yankin tekun Bahar-Rum na daga cikin wadanda suka fi dandana kudarsu a wannan sauyi na zafi da ake gani.
Tsawon kwanaki kasashen Italiya da Sifaniya da Girka suke fama da tsananin zafin.
Ma’aikatar lafiya ta Italiya ta yi gargadi da ankarar da jama’a gama illoli da matakan da ya kamata su dauka, domin kariya, a biranen kasar 16, wadanda suka hada da babban birni, Rum da Bologna da Florence.
Kuma hukumomin kasar suna ganin matsalar za ta ci gaba har wannan satin da za a shiga, inda yanayin zafin zai iya kai wa maki 48 a ma’aunin Selshiyas a birnin Sardinia, kamar yadda aka ruwaito a kafafen watsa labaran kasar ta Italiya.
Haka kuma ake ganin lamarin zai kasance a sauran sassan kudancin Turai.
Masanin kimiyyar sifa, kuma tsohon ministan makamashi na Italiya Roberto Cingolani ya gaya wa BBC cewa halin da ke ciki ya sa mutane sun fara fahimtar alakar tsananin sauyin yanayin da ke faruwa da kuma dumamar yanayi a duniya;
Ya ce, tsawon shekaru ana raina matsalar sauyin yanayi da dumamar yanayi – yanzu mun makara.
Ina ganin yawancin gwamnatoci a yanzu suna aiki sosai su rage tasirin sauyin yanayi. To amma tun da wannan kamar wani yanayi ne ake na gaggawa, sai ya kasance muna ta fama kawai.
Masanin ya kara da cewa, ba ruwan yanayi na duniya da siyasa da wata yarjejeniya da kuma kutungwilar mutane. Ita duniya tana gudana ne yadda take a tsare.
‘’Kuma ina ganin yanzu mun yarda ba wani kokwanto cewa abubuwa na sauyawa, wanda dole kowa ya tashi tsaye ya yi wani abu’’ in ji shi.
Ya kara da cewa ; ‘’A don haka ina ganin watakila duniya za ta koya mana darasi dukkaninmu cewa sai mun kara himma.’’
Haka ake ganin tsananin zafin zai ci gaba ya kai matakin da ba a taba kaiwa ba a sauran sassan Turan ba tare da ganin alamar sauki ba a cikin makon mai shigowa.
A Sifaniya zafin ya haddasa gobarar daji a tsibirin La Palma, da ke kusa da gabar tekun Afirka, inda aka kwashe akalla mutum dubu biyu yayin da wutar ke ci ganga-ganga.
Ita ma Moroko a bangaren Afirka na wannan yanki na tekun bahar-Rum ta shiga rukunin da hukumomi ke yi wa jama’a gargadi a kan tsananin zafin
Haka ita ma Amurka, wadda kashi daya bisa uku na al’ummarta ke cikin tsananin zafin, can a yankinta na kudu maso yamma ana fama da zafin sosai, inda a birnin Phoenix, zafin ya wuce maki 43 a ma’aunin Selshiyas, sama da mako biyu.
Hukumomi na gargadin mutane da cewa duk wanda ba shi da wani tanadi kyakkyawa na na’urar sanyaya muhallinsa ko wadata kai da isasshen ruwa to fa yana cikin hadari.
Jamus, ma abin mamaki ba ta tsira daga matsalar ba ta tsananin zafi, inda ‘yan siyasa suka bi sahu na gargadin cewa bala’in sauyin yanayi tuni ya fara hallaka jama’a.
Wasu sassan kasar China da Japan su ma ba su tsira ba daga yanayin na tsananin zafin.