BBC Hausa of Sunday, 11 June 2023

Source: BBC

West Ham na farautar 'yan wasa, Chelsea na tattaunawa kan Lavia

Hoton alama Hoton alama

West Ham na son cimma yarjejeniya da dan wasan Arsenal Emile Smith Rowe mai shekara 22, idan Declan Rice ya yanke hukuncin tafiya Arsenal. (Sun)

Ajax na neman fam miliyan 45 kan ɗan wasansu na Mexico mai buga tsakiya Edson Alvarez, wanda ake raɗe-raɗin West Ham na son maye gurbin Rice da shi. (Guardian)

Bayern Munich ita ma na zawarcin ɗan wasan na West Ham Rice sai dai kamar yadda rahotanni ke nunawa Arsenal ce babu mamaki za ta yi fintinkau. (Sky Sport Germany, in German)

Manchester City ta tattauna da RB Leipzig kan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 21. (Football Insider)

Ana samun ci gaba a tattaunawa tsakanin Arsenal da Joao Cancelo, sai dai kuma Manchester City na son fam miliyan 45 kan ɗan wasan mai shekara 29. (FootballTransfers)

Kocin Manchester United Erik ten Hag ya datse kokarin Eintracht Frankfurt na saye Victor Lindelof a wannan kaka. (Bild, via Metro)

Chelsea na tattaunawa da Southampton kan ɗan wasanta Romeo Lavia, mai shekara 19. (Football London)

Mai tsaron raga a Inter Milan asalin kasar Kamaru Andre Onana ya cimma yarjejeniya da Chelsea, amma inter tayi watsi da kuɗin da aka gabatar kansa na fam miliyan 34. (Tuttomercatoweb, in Italian)

Chelsea ta kuma kwaɗaitu da ɗan wasan AC Milan, Mike Maignan, mai shekara 27. (L'Equipe, in French - subscription needed)

Luton Town na tattaunawa da mai tsaron raga a Bosnia Asmir Begovic, mai shekara 35, wanda ya baro Everton. (Telegraph - subscription needed)

Crystal Palace da Fulham za su gabatar da tayi kan ɗan wasan Coventry City da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 25. (Football Insider)

Chelsea na jiran ta gani ko AC Milan za ta kulla yarjejeniyar da take magana na fam miliyan 15 kan ɗan wasan ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 27, bayan korar Paolo Maldini da Frederic Massara. (Telegraph - subscription needed)

Kungiyar Al-Ahli ta Saudiyya ta shirya gabatar da tayi fam miliyan 40 duk shekara kan ɗan wasan Algeria Riyad Mahrez, mai shekara 32, idan zai bar Manchester City a wannan kaka. (Mirror)

Tottenham da Manchester United sun shirya hakura da cinikin David Raya idan Brentford ba ta rage kuɗin da take nema kan ɗan wasan mai shekara 27 ba, wato fam miliyan 40. (Standard)