Ƙungiyar West Ham na son ta karbi aron Harry Maguire daga Manchester United. (Telegraph)
Mai yuwuwa Barcelona da Manchester City su yi musayar 'yan wasa biyu a tsakaninsu, inda Frenkie de Jong, zai je City, Bernardo Silva ya je Barca. (Mirror)
Daya daga cikin manyan shugabannin Bayern Munich, Uli Hoeness ya yi amanna Harry Kane, zai bar Tottenham ya koma wajen zakarun na Jamus a bazaran nan. (kicker)
A dangane da rashin tabbas na makomar Kane din Tottenham Hotspur ta fara zawarcin matashin dan wasan Juventus Dusan Vlahovic, dan Serbia mai shekara 22. (Rudy Galetti)
Rahotanni na cewa Newcastle United ta gabatar da tayin fam miliyan 82 a kan matashin dan wasan gaba na gefe na Napoli Khvicha Kvaratskhelia, dan Georgia. (Express)
Wolves ta shirya gabatar da tayin sama da fam miliyan 20 a kan dan wasan tsakiya na Bristol City Alex Scott, na Ingila mai shekara 19. (Telegraph )
Sakamakon tayin da Liverpool ta samu na fam miliyan 40 a kan dan wasanta na tsakiya Fabinho, na Brazil, daga Al-Ittihad ta Saudiyya, kungiyar ba ta tafi da shi wasannin sansanin shirya tunkarar kaka mai zuwa ba a Jamus. (Daily Star)
Shi kuwa kyaftin din Liverpool din Jordan Henderson ya cimma matsaya da kungiyar Al Ettifaq ta Saudiyyar, to amma su kuwa kungiyoyin biyu ba su kammala cinikin ba zuwa yanzu. (Fabrizio Romano)
Pierre-Emerick Aubameyang ya yarda ya bar Chelsea zuwa Marseille, inda ya amince a rage yawan albashinsa domin cinikin ya tabbata. (GOAL France)
Leicester City na duba yuwuwar karbar aron dan wasan tsakiya na Italiya Cesare Casadei, mai shekara 20 daga Chelsea. (Mail)
Manchester City da Al Ahli ta Saudiyya na ci gaba da tattaunawa a kan Riyad Mahrez, dan Algeria. (Fabrizio Romano)
Haka shi ma dan gaban Newcastle Allan Saint-Maximin, dan Faransa, kungiyar ta Al Ahli tana sonshi. (Alkass )
Inter Milan ta hakura da zawarcin Romelu Lukaku, inda a yanzu ake ganin dan wasan na Chelsea, dan Belgium kila ya tafi ko dai Saudiyya ko kuma Juventus. (Fabrizio Romano)
Ga alama dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Jonjo Shelvey, ya kusa barin kungiyar ganin cewa ba ta tafi da shi sansanin atisayen shirya wa kaka mai zuwa ba. (The Athletic)
Sheffield United da ta samu ci gaba da zuwa gasar Premier ce aka ce take shirin sayen dan wasan dan Ingila. (The Mirror)
Juventus na zawarcin dan wasan tsakiya na Barcelona, Franck Kessie, na Ivory Coast mai shekara 26. (Fabrizio Romano)
Tsohon dan wasan tsakiya na Leicester City Danny Drinkwater, ya ce yana son sake komawa kungiyar bayan ya bar ta zuwa Chelsea shekara shida. (The Mirror)