Wolves ta sake ɗaukar ɗan wasan baya na Jamhuriyar Ireland Matt Doherty a kan kwantiragin shekara uku.
Doherty ya bar Wolves zuwa Tottenham a 2020, amma bai samu yadda yake so ba, sai ya koma Atletico Madrid a watan Janairu.
Ɗan wasan mai shekara 31 ya buga wasa biyu kacal a Atletico, sannan ya koma Molineux a kyauta.
Doherty ya buga wa Wolves wasa 302 a karon farko tsakanin 2010 zuwa 2020, inda ya ci ƙwallo 28.
Ɗan wasan na Jamhuriyar Ireland ya buga duk wasannin Premier League na Wolves' a kakar 2018-19, kuma ya taimaka wa ƙungiyar Nuno Espirito Santo zuwa matsayi na bakwai shekara biyu a jere.
Yana cikin tawagar Wolves da ta kai wasan daf da kusa da ƙarshe a gasar cin kofin Europa a shekarar 2019-20.
Ɗan wasan bayan ya zama ɗan ƙwallo na bakwai da Wolves ta saya da bazara yayin da Julen Lopetegui ke ƙoƙarin sake fasalin ƙungiyar bayan kammala gasar Premier a mataki na 13 bara.