BBC Hausa of Thursday, 4 May 2023

Source: BBC

Yadda aka karbo mutum 75 daga hannun 'yan bindiga a Zamfara

Mazauna kauyukan Zamfara na yawan biyan kudi ga ‘yan fashi domin samun zaman lafiya Mazauna kauyukan Zamfara na yawan biyan kudi ga ‘yan fashi domin samun zaman lafiya

A cikin daren Juma'a ne iyayen yara a garin Wanzamai na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara suka karbo kimanin yara 70 daga cikin mutum 95 da 'yan bindiga suka sace makwanni uku da suka gabata.

Mutanen da aka karbo sun hada da maza da mata wadanda akasarinsu matasa ne masu shekaru kasa da 20 da yara 'yan kasa da shekara 10 da kuma dattawa hudu.

Tun bayan sace mutanen ne al'ummar garin na Wanzamai suka fara neman hanyar da za su bi wajen ceto mutanen nasu.

Daya daga cikin mutanen garin da ya bukaci BBC ta sakaya sunansa ya ce wadanda aka sako sun kanjame sun koma kamar kwarangwal.

Ya kara da cewa Allah ne Ya karbi addu'o'insu saboda akwai gidaje da aka daukar wa mutane hudu har zuwa goma.

Mutumin ya kuma nuna farin ciki inda ya ce karbo mutanen ya faranta wa dukkan 'yan garin rai.

Shi ma daya daga cikin iyayen yaran da aka karbo wanda BBC ta boye sunansa ya ce sai da suka biya kudade kafun aka ba su 'ya'yan nasu.

"Sai da wasunmu suka sayar da gidajensu, wasu kuma gonaki sannan wasu kuwa sai da aka yi bara aka tara kudi aka kai wa 'yan bindigar kafun suka sako su" in ji shi.

Dattijon ya kara da cewa barayin mutanen sun kashe matasa maza biyu daga cikin wadanda aka kama ranar Sallah.

Ya kara da cewa a halin yanzu yaran da kuma sauran mutanen da aka karbo din suna asibiti inda ake duba lafiyarsu.

An sace mutanen ne da adadinsu ya kai 95 yayin da suka je aikin gona a garin na Wanzamai.

Ya zuwa yanzu a kwai mutum 25 a hannun 'yan bindigar a cewar 'yan uwan wadanda aka sace din.

Aukuwar wannan lamari na garin Wanzamai na jihar Zamfara karin manuniya ce, game da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da addabar jama'a a jihar.