BBC Hausa of Monday, 24 July 2023

Source: BBC

Yadda ƴan ci-rani ke jefa rayuwarsu cikin hatsari wajen tsallaka teku

'Yan ci-rani a tekun Bahar Rum 'Yan ci-rani a tekun Bahar Rum

'Yan ci-ranin da aka kubutar a daya daga aikin ceto 'yan ci-rani a tekun Bahar Rum da aka yi, sun ce babu abin da zai hana su cimma burinsu na kokarin shiga Turai.

An ceto 'yan ci-ranin ne bayan da wasu daruruwa suka mutu, sakamakon nutsewar jriginsu a tekun Girka.

Sun shaida wa BBC cewa babu abin da zai dakatar da su daga yunkurin na isa Turai.

Masu aikin ceto daga gidauniyar 'SOS Mediterranée' na ci gaba da sintiri a kan jiragen ruwa sanye da hulunan kwano da rigunan fito, domin ci gaba da tsamo 'yan ci-ranin da kwale-kwalensu ya samu matsala.

'Yan ci-ranin waɗanda mafi yawansu matasa ne maza da mata, galibi da suka fito daga ƙasar Gambiya, sun shafe sa'a 15 a cikin teku, inda suka shafe gomman kilomita daga garin Castelverde na kasar Libya.

Mutanen sun sha baƙar wahala, kuma suna cikin tsananin buƙatar taimako.

Wasu daga cikinsu sun shaida wa BBC cewa kafin zuwan masu aikin ceton, sai da aka fara faɗa kan batun tsayar da jirgin.

Wasu sun ce a ci gaba da tafiya, yayin da wasu ke kiran da a hakura da tafiyar, daga baya a ƙara gwadawa, a cikin wannan cacar-bakan ne wayar wani ta faɗa ruwa.

Kaɗan ne daga cikinsu ke guzurin abinci da ruwan sha. Da yawa daga ciki ba su iya amfani da tib domin yin iyo idan an samu matsala a cikin ruwan ba.

An samu firgici a lokacin aikin ceton yayin da masu gadin tekun Libya suka hallara domin taimakawa.

Tarayyar Turai ce dai ta taimaka wajen samar da jirajen tare da horas da ma'aikatan da kuma ɗaukar nauyin aikin ceton.

Da yawa daga cikin 'yan ci-ranin ba wannan ne karonsu na farko da suka taɓa irin wannan tafiya mai cike da hatsari ba.

Wasu daga cikinsu sun yi ta murna a lokacin da jiragen ceton suka kubutar da su, wani daga ciki ya ɗauko wayarsa inda ya rika daukar kansa hoto.

Daga baya wani daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa a lokacin da masu aikin ceto suka tsamo shi daga cikin tekun ya yi tunanin cewar ''ya isa Turai''.

'Yan ci-ranin sun yi gaggawar shiga babban jirgin masu aikin ceton 'Ocean Viking', inda ake duba lafiyarsu tare da sake musu tufafi da sauran kayayyakin bukata irin su man shafawa da man goge baki.

Gidauniyar ta ankarar da hukumomin Italiya, waɗanda suka sanar da birnin Bari da ke kudancin ƙasar a matsayin wata matattara da ake tara 'yan ci-ranin da aka ceto.

Hakan ya biyo bayan sabuwar dokar da ta buƙaci duk jirgin ruwan da ya ceto 'yan ci-rani da ya nufi birnin domin kai su, maimakon ci gaba da neman ƙarin wasu.

Birnin na Bari na da nisan tafiyar kwana uku daga Tekun.

A yayin da muka yi shirin shiga jirgin, mun tattauana da wasu 'yan ci-ranin a dakin da ake duba lafiyarsu a cikin jirgin.

Da yawa sun shaida wa BBC cewa suna sane da irin hatsarin da ke tattare da wannan tafiyar.

Haka kuma da dama sun ce wannan ba shi ne karonsu na farko na yunkurin shiga Turai ba.

Sun ce a lokuta da dama sun sha tsallake rijiya-da-baya, inda masu aikin ceto suka kubutar da su, inda aka mayar da su Libya.

"Sau bakwai ina yunkurin tafiya Turai ta wannan hanya," kamar yadda wani matasi mai shekara 17 ya bayyana.

Kowanne dan ci-ranin da BBC ta tattauna da shi ya ce yana da abokin da ya mutu a yunkurin da ya yi a irin wannan tafiya.

Wasu daga cikinsu na bibiyar labarai a shafukan sada zumunta, musamman labarin bala'in da ya afku da 'yan ci-rani a tekun Girka, cikin makonnin da suka wuce, inda akalla mutum 750 suka mutu.

Waɗanda su ma suka taso daga kasar Libya.

Daya daga cikinsu ya ce mutawar waɗancan 'yan ci-ranin ba ta hana shi yunkuri nasa ba, saboda a cewarsa tasu ce ta zo da haka.

"Dama ɗayan biyu ne, ko Turai ko mutuwa a teku,'' kamar yadda wani matashin ya shaida wa BBC.

Fiye da kashi 80 cikin 100 na mutanen da aka kubutar yara ne 'yan ƙasa da shekara 18.

Da yawa daga cikinsu sun bar gidajen iyayensu shekaru da suka wuce da niyyar zuwa Turai don nemo kuɗin da za su riƙa aika wa danginsu.

Da yawa sun ce ɗaya daga cikin iyayensu, ko ma duka iyayen nasu sun rasu, kuma kasancewarsu manya a gidan ɗawainiyar kula da 'yan uwansu ta koma kansu.

'Yan Gambiya ne suka fi yawa cikin 'yan ci-ranin

Mafi yawansu daga Gambiya suke, fiye da mil 2,000 daga kudu maso yammacin Libya.

Gambiya na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da talauci ya yi wa katutu, kuma Hukumar Kula da Kaurar Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta ce a shekarun baya-bayan nan 'yan Gambiya sun fi 'yan kowacce ƙasa a nahiyar Afirka yin kaura.

Hukumar ta ce daga 2015 zuwa 2022, fiye da 'yan Gambiya 64,000 ne suka tsallaka Turai ta ɓarauniyar hanya.

Wani matashin mai suna Suma mai shekara 18 ya ce ya fara tafiyarsa ne bayan shi da wakilinsa sun tsara yadda tafiyar za ta kasance daga kusa da Mali, tun da farko sun tsara tafiya tare da wakilin nasa, inda suka bi ta Algeriya sannan zuwa Libya.

Ya ce mutanen da suka yi safararsa ta ɓarauniyar hanyar sun azabtar da shi, ta hanyar duka, sannan suka hana shi abinci.

To sai dai a cikin jirgin BBC ba ta ga mutumin da ya ce sun yi tafiyar tare ba, don haka BBC ba za ta iya tabbatar da ikirarin nasa ba.

Da yawan mutanen da aka ceton babu abin da suka mallaka in banda tufafin da ke jikinsu, kowa na barin jakarsa ne a Libya.

Sun ce a Libya suna zama ne a wasu ɗakunan da masu fasa ƙwaurin mutanen suka tanada, inda suke tatsarsu kuɗaɗe masu yawa domin zama a ɗakunan.

'Yan ci-ranin sun ce sukan kashe sama da dala 570 wajen tsallakawa zuwan Turan.

Kawun Suma ya aika masa da wasu kudi a lokacin da yake Libya.

Haka su ma wasu 'yan ci-ranin sun ce danginsu kan ci bashi mai yawa domin aika musu kuɗi a lokutan da suka makale a Libya.

Da yawa cikinsu sun ce sun kwashe watanni tsare a gidan cibiyoyin tsare 'yan ci-ranin Libya.

Bayan da jami'an tsaron tekun Libyan suka kama su, a lokacin da suke yunkurin tsallakawa.

Idan suka samu kudin da za su ishe su biya domin tsallakawa da su, yan ci-ranin sukan tunkari wakilansu domin tsara yadda tafiyar za ta kasance.

Waɗanda a cewar Suma ba abin yadda ba ne, domin kuwa ''abin da za su faɗa maka daban, abin da kuma za su yi maka daban'' a cewarsa.

Ya ce a baya wakilan sun shaida masa cewa za a tsallaka da shi a jirgin da zai ɗauki fasinjoji 55 zuwa 60, amma sai ga shi a cikin jirgin da ake hura wa iska tare da mutum sama da 90 ke cikinsa.

''Don haka dole ka yarda ba ka da wata jayayya, dole ka fawwala komai zuwa ga Ubangiji'', in ji shi.

Adama ya ce yana ɗaya daga cikin mutum 125 da suka nutse a jirgin da suke ciki, kuma yana ɗaya daga cikin mutum 94 da suka tsira da ransu.

"Ina kallon abokina ya mutu. Na taimaka wa da dama daga cikinsu, to amma ba zan iya taimakon duka abokan nawa ba, ina kallonsu ruwa na tafiya da su.''

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Doinkin Duniya ta ce fiye da mutum 64,000 ne suka isa Italiya a wannan shekara, bayan da suka tsallaka tekun Bahar Rum.

Kume fiye da mutum 10,000 daga cikinsu daga Gambiya suke.

Matasan sun shida wa BBC cewa suna kallon Turai a matsayin wuri mai inganci da tsaro da kwanciyar hankali ta fuskar rayuwa, inda za su koma makaranta, sannan su samu aiki mai kyau.

Sara Mancinelli, jami'a a hukumar bayar da agaji ta Red Cross ta shaida wa BBC cewa 'yancin da 'yan ci-ranin ke da shi na zama a Turai ya danganta da irin niyyar da kowanne ya je da ita.

"Ko da ba a yaƙi da ko muzgunawa a ƙasashensu, za su iya samun izinin zama da samun kariya ta wasu dalilan'', kamar yadda jami'ar ta bayyana.

Chiara Cardoletti, wakiliyar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sakamakon yawan tuɗaɗar 'yan ci-ranin zuwa Italiya, a yanzu kasar ba za ta iya ɗaukar ɗawainiyar bukatun 'yan ci-ranin ba.

A yayin da yake daf da sanya ƙafarsa a Turai, murnar Suma ta koma ciki yayin da muka yi ban kwana da shi a lokacin da jirgin cetonsu ya koma Libya.