BBC Hausa of Thursday, 20 October 2022

Source: BBC

Yadda 'yan sandan Najeriya suka tarwatsa masu tunawa da zanga-zangar EndSars

Yan zanga-zanga ta EndSars Yan zanga-zanga ta EndSars

‘Yan sanda a Legas da ke kudancin Najeriya sun tarwasa matasa fiye da 500 ranar Alhamis da suka taru domin tunawa da zanga-zangar nan ta kawo karshen jami’an rundunar ‘yan sanda ta SARS, da aka yi wa lakabi da EndSars a ranar 20 ga watan Oktoban 2020 a mashigar Lekki. Daruruwan ‘yan Najeriya ne suka taru a mashigar ta Lekki rike da alluna da kwalaye, inda suke rera wakokin kin jinin gwamnati da kuma neman a bi musu hakkokinsu. Wasu kuma sun yi ta daga tutocin Najeriya da jini a jikinsu da zimmar tunawa da wadanda suka rasu, a cewar matasan. Matasan Najeriya da dama sun yi ta yada batun tunawa da zanga-zangar ta EndSars bayan shekara biyu a kafofin sada zumunta da kuma tunawa da wadanda ake zargin an kashe a zanga-zangar da ta girgiza ƙasar. A watan Oktoban 2020 ne matasa suka fito kan tituna a fadin ƙasar domin nuna adawa da cin zarafi da kuma kashe mutane da jami’an rundunar ‘yan sanda ta SARS ke yi a lokacin, inda suke son a rusa rundunar. Sun kuma zargi jami’an SARS da musgunawa ‘yan ƙasar musamman ma matasa. Matasan sun dai shafe tsawon kwanaki suna zanga-zangar, inda suka toshe wasu manyan hanyoyi har da Abuja babban birnin ƙasar. Zanga-zangar ta lumana ta rikide zuwa tarzoma bayan da ake zargin wasu da ‘yan daba da karbe ikonta, inda suka fara lalata kayakin jama’a da kuma ta kai har ga rasa rai. ‘Yan sandan ƙasar ma sun fito sun bayyana cewa an kashe wasu jami’ansu a tarzomar. A ranar 19 ga watan Oktoban 2022, wani mawakin ƙasar mai suna Falz, ya wallafa a shafinsa na instagram cewa za su fito tattaki a mashigar Lekki domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda suka yi a shekara ta 2021. An kuma tsara yin tattakin a wasu jihohi a fadin ƙasar. Batun tunawa da zanga-zangar EndSARS dai ya kasance abin da aka fi tattaunawa a shafin tuwita a Najeriya a safiyar yau Alhamis. Mutane sun yi ta rubuta ‘Ba zamu manta ba’’, a shafukansu na tuwita domin tunawa da ranar. Bayan faruwar zanga-zangar, gwamnatoci daban-daban kama daga jihohin Legas da Ribas da kuma Osun, sun kafa kwamitoci domin gudanar da bincike kan abin da ya janyo matasan ƙasar suka bazama kan tituna, inda bayan jin bahasi na tsawon watanni, kwamitin ya bayar da shawar biyan wadanda zanga-zangar ta shafa diyya. Me ya faru a Mashigar Lekki? Wasu masu zanga-zanga da wadanda ta shafa sun bayyana cewa mutane da dama ne suka mutu a mashigar Lekki, sai dai, gwamnatin Najeriya ta ce babu wanda ya rasa ransa. Ministan ƴada labarai, Lai Muhammad, ya bayyana a lokacin cewa ‘ta ya ya za a yi kisan ƙiyashi ba tare da ganin gawar wanda ya mutu ba’. Sojojin ƙasar sun amince da cewa sun yi harbe-harbe a Mashigar ta Lekki lokacin zanga-zangar, amma sun ce basu kashe kowa ba. Gwamnatin Amurka ta ce ba za ta yi magana ba kan yawan mutane da aka kashe a zanga-zangar ta EndSARS. A wata sanarwa da gwamnatin ta Amurka ta fitar, sun bayyana cewa da gaske wasu jami’an tsaro sun ayyana dokar takaita zirga-zirga a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, inda suka yi ta harbi a sama domin tarwasa masu zanga-zanga da suka taru a Mashigar Lekki na jihar Legas wadanda suka taru domin son a rushe jami’an rundunar ‘yan sanda ta SARS bayan zarginsu da cin zarafi. A wata sanarwa da gwamnatin ta Amurka ta fitar, sun bayyana cewa da gaske wasu jami’an tsaro sun ayyana dokar takaita zirga-zirga a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, inda suka yi ta harbi a sama domin tarwasa masu zanga-zanga da suka taru a Mashigar Lekki na jihar Legas wadanda suka taru domin son a rushe jami’an rundunar ‘yan sanda ta SARS bayan zarginsu da cin zarafi. Duk da cewa gwamnati ta amince cewa sojoji sun yi harbe-harbe a Lekki a daren da aka gudanar da zanga-zangar, amma sun ce mutum biyu ne kadai suka mutu a wajen. Sai dai, alkaluman sun yi sabani da rahoton Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Amnesty International wanda ya nuna cewa mutum 10 ne suka mutu. Amma babu kungiyar da ta fito ta nuna amincewa da alkaluman na Amnesty.