BBC Hausa of Friday, 14 October 2022

Source: BBC

Yadda zaman fargaba ke karuwa a Yammacin Kogin Jordan

Wasu sojojin Jordan Wasu sojojin Jordan

Dubban Falasdinawa na cikin matsi kan tsauraran dokokin tafiye-tafiye da sojojin Isra’ila suka kakaba musu a wasu sassan Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Kudus. Hakan na zuwa ne bayan barkewar sabon rikici a fadin yankunan da Isra’ilan ta yi wa ƙawanya. A tsawon mako da ya gabata, sojojin Isra’ila sun kashe wasu matasan Falasdinawa biyar, inda Falasdinawan kuma suka harbe sojojin Isra’ila biyu. Sojojin na Isra’ila dai sun sha alwashin ci gaba da bincike domin gano ‘yan bindingar da suka kashe sojojin nasu. Sai dai, Falasdinawan sun ce yawan yankunan da sojojin Isra’ilan ke rufewa ya fara sanya su cikin matsi. Yawancin mazauna Shuafat – wani babban sansanin ‘yan gudun hijira da sojojin Isra’ila suka raba da birnin – sun samu damar ficewa tun ranar Asabar da daddare, lokacin da wani Bafalasdine rike da karamar bindiga ya harbe sojan Isra’ila mai shekara 18 a shingen binciken sojoji. Tarzoma ta barke cikin dare tsakanin sojojin Isra’ila da kuma Falasdinawa, inda ake faragbar cewa rikicen zai iya watsuwa zuwa sauran wurare. Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Tor Wennesland, a makon nan ya yi gargadi kan tabarbarewar al’amuran tsaro wanda kuma ke kara sanya tsoro da kuma kiyayya tsakanin jama’a. A ranar Laraba da dare, sojojin Isra’ila suka harba hayaki mai sa ƙwalla kan Falasdinawa masu zanga-zanga, inda su kuma suka yi ta jifan sojojin da duwatsu da kuma bam din fetur a gabashin Birnin Kudus. Yankuna da ke makwabtaka da birnin sun fuskanci irin wannan tarzoma ta cikin dare da ta barke ta tsawon makonni a watan Mayun bara, wanda ya sanya rikicin ya fadada. An ruwaito cewa Isra’ilawa rufe da fuskokinsu sun yi ta jifan duwatsu a kan masallaci a wani yanki, a wani wajen kuma ‘yan sandan sun ce Falasdinawa sun harba duwatsu kan wata mota dauke da iyalan Yahudawa. A garin Huwara da ke yamma da Kogin Jordan, hoton bidiyo ya nuna Isra’ila ‘yan kama wuri zauna rufe da fuskokinsu na dauke da sanduna, inda suke farwa shagunan Falasdinawa, yayin da sojoji kuma ke kallo ba tare da daukar mataki ba. ‘Aikin ta’addanci’ Jami’an tsaron Isra’ila sun yi ta kutsawa gidaje a garin Shuafat, domin neman dan bindigar da ya kai hari na ranar Asabar, inda suka toshe garin ba shiga ba fita na tsawon kwanaki shida. Wani lauya Bafalasdine mai suna Medhat Debeh, da ke zama cikin sansanin, ya bayyana cewa mutane sun shiga cikin dogayen layuka don samun damar fita daga garin a ranar Alhamis. Ya ce an bude hanya na kankanin lokaci da safe domin farantawa jami’an diflomasiyya na kasashen waje. "Akwai mutane da ke fama da cutuka da kuma ciwonsu ya yi tsanani saboda na ki bari a yi musu magani,’’ in ji lauyan yayin tattaunawa da BBC. A ranar Laraba, ministan tsaron Isra’ila, Benny Gantz, ya ce sojoji za su fadada ayyukansu domin nemo wadanda suka kashe sojojin. "Za mu kama ‘yan ta’addan da kuma wadanda suka turo su, za mu kuma hukunta su," in ji ministan. A ranar Laraba, ma’aikatar lafiya ta Falasdinu, ta sanar da mutuwar wani Bafalasdine dan shekara 18 wanda sojojin Isra’ila suka harbe a sansanin al-Aroub kusa da birnin Hebron. Sojojin sun ce sun bude wuta ne ga Falasdinawa da ke jifa duwatsu kan motoci, sai dai ba ta ce me ya sa aka yi amfani da karfi wajen dakatar da su ba. A farkon makon nan, wani dan bindiga Bafalasdine ya harbe sojan Isra’ila kusa da wani matsuguni na Yahudawa da ke birnin Nablus. Karuwar tarzoma Ana ci gaba da samun karuwar tarzoma a arewacin Kogin Jordan a wannan shekara a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke kutsawa gidajen Falasdinawa da kuma barazanar tsaro da ake fuskanta a biranen na Falasdinawa. A ranar Alhamis, sojojin Isra’ila suka ci gaba da toshe hanyoyi a Nablus, yayin da ake samun rahotannin takaita zirga-zirga ga Falasdinawa a kusa da birnin Huwara. Wani shaida ya fadawa BBC cewa mutane sun kasance cikin dogayen layuka a shingen bincike na sa’o’i da dama domin samun fita daga yankin. A ranakun 7 da kuma 8 ga watan Oktoba, sojojin Isra’ila suka kashe matasan Falasdinawa guda hudu yayin wani rikici na sa’a 24 a Yamma da Kogin Jordan. Wadanda aka kashen sun hada da wani yaro mai shekara 14. Sojojin sun yi ikirarin cewa an bude wuta ne ga Falasdinawan saboda harba bam na fetur a kan motoci. A ranar Litinin ma, wani yaro Bafalasdine mai shekara 12 ya rasu bayan fama da  raunukan harbi lokacin da Isra’ila suka kai samame a birnin Jenin a watan Satumba. A wannan shekara, sama da Falasdinawa 100 aka kashe a Yammacin Kogin Jordan bayan da sojojin Isra’ila suka zafafa samamen bincike da kuma kame, bayan wata mummunar tarzoma da Falasdinawa suka yi kan Isra’ilawa wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 18 a tarzomar.