Kimanin 'yan wasa 12 daga Real Madrid aka gayyata zuwa tawagoginsu domin buga wasannin neman shiga gasar Nahiyar Tura,i ko ta kofin duniya.
Bayan haka a wannan lokacin za a buga wasannin sada zumunta da kuma na neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka.
Cikin 'yan wasan sun hada da Bellingham, Carvajal, Joselu, Kepa, Modrić, Tchouameni, Camavinga, Alaba, Rüdiger, Rodrygo, Valverde da kuma Lunin.
Jerin 'yan wasan da tawagoginsu:
Carvajal, Joselu da kuma Kepa (Sifaniya), Bellingham (Ingila), Camavinga da Tchouameni (Faransa), Alaba (Austria), Rudiger (Jamus), Modric (Croatia), Lunin (Ukraine), Rodrygo (Brazil) da kuma Valverde (Uruguay).
Ga jerin wasannin da kasashen za su buga
Sifaniya
Carvajal, Joselu da Kepa za su buga wa Sifaniya wasannin neman gurbin shiga gasar nahiyar Turai.
Faransa
Camavinga da Tchouameni za su buga wa Faransa karawar neman shiga gasar kofin nahiyar Turai, shi kuwa Rudiger zai wakilci Jamus.
Austria
David Alaba zai yi wa Australia wasan sada zumunta da na neman shiga gasar nahiyar Turai.
Croatia
Kyaftin Modric zai buga wa Croatia wasa biyu da za ta kara a neman shiga gasar nahiyar Turai.
Ingila
Bellingham zai buga wa Ingila wasan neman shiga gasar nahiyar Turai da kuma na sada zumunta.
Jamus
Rudiger zai buga wasan sada zumunta biyu da Jamus za ta kara da Japan da kuma Faransa, yayin da Camavinga da Tchouameni za su yiwa Faransa tamaula.
Ukraine
Ukraine ta gayyaci Lunin domin buga mata wasa biyu a neman shiga gasar kofin nahiyar Turai da za ta kara da Ingila da kuma Italiya.
Brazil
Rodrygo zai yiwa Brazil wasa biyu da za ta buga domin neman gurbin shiga gasar kofin duniya da za a buga a 2026.
Uruguay
Fede Valverde zai buga wa Uruguay wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Chile da kuma Ecuador.