Liverpool za ta ziyarci Real Madrid domin buga wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Zakarun Turai da za su kara a filin wasa na Alfredo Di Stefano.
Kungiyoyin biyu sun lashe kofin Champions League 19 a tsakaninsu, inda Real Madrid take da 13, ita kuwa Liverpool ta dauki guda shida.
Real Madrid ta lashe kofi na 13 ne a kakar 2017/18 lokacin da ta doke Liverpool a wasan karshe da ci 3-1 da suka kara a birnin Kiev a Ukraine.
Real Madrid da Liverpool sun kara a gasar Zakarun Turai ta Champions League da ta Europa sau shida, inda kowacce ta yi nasara a wasa uku-uku.
Sai dai a kakar bana Real Madrid da Liverpool na fuskantar kalubale, bayan da Real ke harin lashe Champions League wanda shi ne ya rage a gabanta.
Liverpool wadda ta lashe Premier League a bara karo na farko bayan shekara 30 tana ta bakwai a kan teburin bana.
Ita kuwa Real Madrid mai rike da La Liga tana ta uku a kan teburin gasar Spaniya na bana, bayan Atletico ta daya da maki 66, sai Barcelona mai maki 65.
Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan kwallon da za su fuskanci Liverpool a wasan quarter finals a Champions League ranar Talata.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Arribas.
Masu buga gaba: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.