Ranar Litinin Karim Benzema dan kwallon tawagar Faransa ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya da ake kira Ballon d'Or na 2021/22. Dan wasan na Real Madrid shi ne na baya-bayan nan da ya lashe kyautar daga kungiyar Santiago Bernabeu a bikin da French Football kan gudanar. Kyauta ita ce ta 66 da aka yi bikin karrama 'yan wasan tamaula da suka yi fice a duniya da aka yi a Faransa. A karon farko an auna kwazon dan wasa bisa bajintar da ya yi a kakar tamaula, maimakon shekara daya da ake yi a baya. Benzema ya zama na 10 da ya lashe Ballon d'Or daga Real Madrid, bayan da Luka Modric ya dauka a 2018 daga kungiyar. Alfredo Di Stéfano shi ne na farko da ya fara lashe kyautar daga Real Madrid a 1957, sannan ya kara zama zakara a 1959. Raymond Kopa, wanda ya taka leda tare da Di Stéfano, shi ne ya lashe kyautar 1958 na biyu daga Real Madrid, sannan Stefanano da ya dauka karo na biyu a 1959. Sauran 'yan wasan da suka lashe Ballon d'Or a Real Madrid sun hada da Zinedine Zidane a 1998, wanda ya karba daga hannun Ronaldo Nazario na Inter Milan, wanda ya lashe a 1997 da kuma a 2002, wanda ya zama zakara a Real Madrid. Figo ya dauki Ballon d'Or a Real a 2000, sai Michael Owen a 2001 da Cannavaro a 2006 da kuma Kaka a 2007. Shi kuwa Cristiano Ronaldo Ballon d'Or biyar ya dauka a tarihin tamaularsa guda hudu a Real Madrid da daya a Manchester United a 2008 Kyaftin din tawagar Portugal wanda ke wasa a Old Trafford yanzu haka ya lashe a 2013 da 2014 da 2016 da kuma 2017.