BBC Hausa of Thursday, 23 November 2023

Source: BBC

Yau Kotun ƙoli ke yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Nasarawa

Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da David Ombugadu na jam'iyyar PDP Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da David Ombugadu na jam'iyyar PDP

A Najeriya, kotun daukaka kara da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, tana yanke hukuncin game da shari'ar zaben kujerar gwamnan jihar Nasarawa, tsakanin gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC da David Ombugadu na jam'iyyar PDP.

Hakan dai ya biyo bayan kammala sauraren bangarorin masu daukaka kara da na wadanda ake kara, da shaidunsu, tare da rufe karbar duk wasu bayanai ne da kotun ta yi tun a ranar Larabar makon jiya.

Wata sanarwa da kotun ta fitar a ranar Laraba, ta ce yau Alhamis ne za a yanke hukunci kan ƙarar.

A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam'iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.

Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri'a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri'a 283,016.

Sai dai rashin gamsuwa da hakan ne ya sa jam'iyyar PDP da ɗan takararta suka garzaya kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamna, wanda a ranar 2 ga watan Oktoba ta soke nasarar ta gwamna Sule.

Hakan ne ya sanya APC da lauyoyinta suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗauka ƙara da ke Abuja wadda ke zaman yanke hukuncin a yau Alhamsi.