BBC Hausa of Monday, 17 April 2023

Source: BBC

Za a aika ɗumbin kayan wasa ga yaran da girgizar ƙasa ta shafa a Turkiyya

Ali Tekce, wani mai gidan cin abinci daga garin na Beverley Ali Tekce, wani mai gidan cin abinci daga garin na Beverley

An maƙare kwalaye har guda 1,000 da kayan wasa ga yaran da girgizar ƙasa ta shafa a Turkiyya, gudunmawa daga mutanen garin Beverly na gundumar East Yorkshire.

Mutane aƙalla 50,000 ne suka mutu a girgizar ƙasa, wadda ta auku ranar 6 ga watan Fabrairu.

Ali Tekce, wani mai gidan cin abinci daga garin na Beverley a gunduma ta East Yorkshire, da ya rasa iyalansa 10 a bala’in kuma ya shirya ƙaddamar da asusun sayen kayan wasan.

Gangamin tattara kudaden ya kuma tara fan dubu 12 kuma Mr Tecke ya ce mutane taimakon da mutane suka bayar abin a yaba ne’’.

Taron kaddamar da asusun tallafin sayen kayan wasan ga kasar Turkiyya da ya gudana a kasuwar Laraba ta garin Beverley a ranar Lahadi ya samu halartar Jakadan kasar Turkiyya a Birtaniya Koray Ertas, wanda ya yaba wa yunkurin mutanen yankin na tara kudaden.

"[Wadannan kananan yara] sun rasa iyayensu, sun rasa gidajensu, kuma muna godiya cewa mutanen Yorkshire da na Beverley da kungiyoyin bayar da tallafi na yankunan suna aikewa da sakonnin jajensu," Mr Ertas ya bayyana.

Jiragen saman a kamfanin zirga zirgar jiragen sama na kasar Turkiyya ne za su tashi da kwalayen takalman da aka cika da kayan wasan yaran irin su ‘yar tsanar teddy bears, da kananan kyaututtuka, da kayan wasa kwakwalwa da alawoyi zuwa kasar ta Turkiyya nan da kwanaki masu zuwa, a cewar Mr Tekce.

Ya kuma ce taimakon ya wuce yadda muka yi tsammani, ta kuma kara da cewa: "Tallafin ya bamu mamaki. Kananan yara miliyan biyar da dubu dari hudu ne suka rasa gidaje da iyaye da makarantunsu, muna son mu faranta wa wadannan kananan yara.’’