BBC Hausa of Wednesday, 15 November 2023

Source: BBC

Za a binciki Chelsea kan wasu kudi da ta biya lokacin Abromovich

Roman Abramovich Roman Abramovich

Mahukuntan harkar kwallon kafa za su ci gaba da binciken kungiyar Chelsea, kan wani rahoton biyan kudi da aka danganta da tsohon mai kulob din, Roman Abramovich.

Wani rahoto da jaridar Ingilan, Guardian ta samu na dauke da wasu takardu da attajirin dan kasar Rasha ya yi amfani da su, wajen biyan kudade ta kamfaninsa miliyoyin fam ga wasu wakilan 'yan wasa da wasu mutane da ake ganin an yi haka ne, don Chelsea ta amfana.

Hakan kuma ya karya dokar hada-hadar kudin kungiya, matukar ba a sanar da mahukunta ba.

Wani batun kuma zai kara nuna yadda Abromovich, wanda ya mallaki Chelsea tsawon shekara 19, ya gudanar da kungiyar, wadda ta samu nasarori da yawa.

A shekara ta 2022, gwamnatin Burtaniya ta umarci attajirin ya sayar da kulob din, saboda hare-haren da Rasha ta kai wa Ukraine, inda ta ce mai Chelsea yana da huldar kut-da-kut da shugaban Rasha.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila da mai kula da shirya gasar Premier League, dukkansu na bincike a kan ko Chelsea ta karya ka'idar hada-hadar juya kudin kungiyar.

A watan Yuli, hukumar kwallon kafan Turai ta ci tarar Chelsea fam miliyan 8.6, bisa samun ta da laifin karya dokar kashe kudi daidai samu, bayan ta gabatar da rahoton hada-hadar da aka samu kuskure tsakanin 2012 zuwa 2019.

Mai kungiyar Chelsea na yanzu, Todd Boehly, shi ne ya ba da rahoton duk abin da ya faru.

Har yanzu mahukuntan hukumar kwallon kafar Ingila da masu shirya Premier League ba su ce komai game da lamarin ba.