BBC Hausa of Tuesday, 14 November 2023

Source: BBC

Za a gurfanar da Alves kan zargin lalata

Dani Alves Dani Alves

Za a gurfanar da tsohon dan kwallon Brazil da Barcelona, Dani Alves gaban wata kotu a Sifaniya, kan zargin lalata.

Alves, mai shekara 40 yana tsare a kukuku ba tare da bayar da shi beli ba tun daga watan Janairu, bayan da ake zarginsa da cin zarafin wata mata a gidan rawa a Barcelona a cikin Disamba.

Ya musanta zargin da ake masa, wanda ya ce lamarin ya faru ne da amincewarta.

Wata kotu a Barcelona ta ce akwai daililai a kansa da ya kamata ya gurfana kamar yadda masu shigar da kara suka bukata da kuma matar.

Ba a tsayar da ranar da ya kamata a fara sauraren karar ba kawo yanzu.

Tun cikin watan Agusta, wani alkali a Sifaniya ya tuhumi Alaves.

A kasar Sifaniya, idan an samu mutum da laifin fyade da ya hada da cin zarafi, zai iya zaman gidan yari daga shekara hudu zuwa 15.

Alves ya buga wa Barcelona wasa 408 inda ya lashe La Liga shida da Champions League uku, yana kuma cikin tawagar 'yan wasan Brazil da ta lashe kofin duniya a 2022.

Kungiya ta baya-bayan nan da ya buga wa tamaula, Pumas UNAM ta Mexico ta soke kwantiragin da ke tsakaninsu a cikin Janairu lokacin da aka tsare dan wasan.