BBC Hausa of Sunday, 6 November 2022

Source: BBC

Za a kara a wasa na bakwai tsakanin Conte da Klopp

Conte da Klopp Conte da Klopp

Za a buga wasan mako na 15 a gasar Premier League ranar Lahadi, inda Liverpool ta ziyarci Tottenham. Tottenham tana mataki na uku a kan teburin Premier League da maki 26. Ita kuwa Liverpool tana ta tara da maki 16 kawo yanzu. Wasan da suka kara a bara tsakanin Tottenham da Liverpool 2021/2022 Premier League Asabar 7 ga watan Mayun 2022               Liverpool         1 - 1     Tottenham      Premier League Lahadi 19 ga watan Disambar 2021             Tottenham      2 - 2     Liverpool Abin da ya kamata ku sani kan wasa tsakaninsu: Wasan da Tottenham ta doke Liverpool 4-1 a Wembley ranar 22 ga watan Oktoban 2017 shi ne nasarar da ta yi a 21 da ta fuskanci kungiyar Anfield a dukkan fafatawa. Liverpool ta yi nasara biyar daga tara baya da Tottenham da rashin nasara daya. Wasa 10 tsakanin kungiyoyin su kan ci gida wato own goal, karawar da aka fi yin wannan kuskuren kenan. Tottenham Hotspur Tottenham ba ta cin kwallo a minti 45 din farko a wasa shida da ta kara a dukkan fafatawa, an kuma zura mata kwallo a minti na 45 daga fafatawa hudu. Tottenham ta samu maki 10 daga wasan da aka kusan doke ta a karawar da take a kakar nan, ita ce kan gaba da ta anfana da hakan. An buga wasa shida tsakanin Antonio Conte da Jurgen Klopp a Premier League, inda suka yi canjaras hudu, kowanne ya ci wasa daya. Harry Kane ya ci Liverpool kwallo shida - Jamie Vardy ne kan gaba a cin kungiyar Anfield mai takwas a raga. Saura wasa daya Hugo Lloris ya zama na uku daga Faransa da zai yi karawa 350 a Premier League, bayan Sylvain Distin da kuma Nicolas Anelka. Liverpool Liverpool ta barar da maki 20 daga karawa 12 a Premier a bana, wadda ta ci wasa hudu da canjaras hudu da rashin nasara a hudu. Liverpool ta ci wasa da yawa a Champions League, fiye da wanda ta samu nasara a Premier League - ta ci biyar a gasar Zakarun Turai da hudu a Premier. Har yanzu Liverpool ba ta ci babban wasa da ta yi a waje ba a bana, tana fuskantar rashin nasara uku a jere a karon farko tun Fabrairu zuwa Afirilun 2012. Roberto Firmino ya ci Tottenham kwallo biyar daga karawa shida.