Za a bayyana jadawalin Premier League na gasar 2023/23 a ranar Alhamis, 15 ga watan Yunin 2023.
Lokacin ne za a fayyace ranakun da za a buga dukkan karawa 380 da lokutan da za a yi wasannin.
Za a fara kakar Premier League ta 2023/24 ranar Asabar 12 ga watan Agustan 2023 - za kuma a yi wasannin karshe ranar Lahadi 19 ga watan Mayun 2024.
Wannan ce kakar farko da za a fara ba tare da cin karo da tsaiko ba, bayan da cutar korona ta haifar da koma-baya na kaka biyu.
Sannan a kakar nan gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar, wadda Argentina ta lashe a 2022, ta sa aka dakatar da wasannin ana tsaka da gasar.
A wannan kakar babu kungiyar da za ta yi wasa biyu a lokacin hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara.
Haka kuma za a yi hutu a tsakiyar kakar da za a shiga tsakanin 13 zuwa 20 ga watan Janairun 2024.
Haka kuma jadawalin 2023/24 zai kunshi mako 34 da za a yi tataɓurza domin fitar da kungiyar da za ta lashe kofin Premier League.
Idan aka fara kakar bana ranar Asabar 12 ga watan Agusta, zai zama kwana 76 ke nan tsakani da aka kammala kakar da ta wuce ta 2022/23.
Cikin watan Yuni 'yan wasa na hutu, wadanda da yawansu kwantiraginsu zai kare a kungiyoyinsu.
Manchester City ce ta lashe Premier League na 2022/23 na uku a jere kuma na biyar a kaka shida.
Wadanda za su wakilci Ingila a gasar Zakarun Turai a 2023/24 sun hada da City da Arsenal da Manchester United da Newcastle, wadanda za su buga Champions League.
Masu buga Europa League kuwa sun hada da Liverpool da Brighton da kuma West Ham, wadda ta dauki Europa Conference League ranar Laraba.
West Ham ta doke Fiorentina 2-1 a wasan karshe da suka buga a Prague.