BBC Hausa of Friday, 9 June 2023

Source: BBC

Za a tuhumi tsohon shugaban Amurka a kan ɓoye takardun sirrin ƙasa

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

Ana tuhumar tsohon shugaban Amurka, Donald Trump a kan yadda ya riƙe wasu takardun sirrin ƙasa bayan ya bar fadar white house.

Mista Trump, mai shekara 76, yana fuskantar tuhuma bakwai ciki har da riƙe bayanan sirrin ƙasa ba da izini ba, in ji kafofin yaɗa labaran Amurka. Har yanzu dai ba a fitar da tuhume-tuhumen a bainar jama'a ba.

Wannan shi ne karo na biyu da ake tuhumar Trump kuma idan kotu ta same shi da laifi ana iya yi masa ɗauri mafi tsanani na shekara goma a gidan yari.

A yanzu dai yana yaƙin neman zaɓe don komawa fadar White House a shekara ta 2024.

Ƙwararru kan harkokin shari'a sun ce tuhumar ba za ta hana Trump sake tsaya wa takarar shugaban ƙasa ba.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumuntarsa na Truth Social ranar Alhamis, Mista Trump ya ce bai aikata wani laifi ba kuma an ba shi sammaci don ya bayyana a wata kotun tarayya da ke Maimi a jihar Florida ranar Talata, inda za a kama shi kafin ya ji tuhume-tuhumen da ake yi masa.

"Ban taɓa tunanin abu ne mai yiwuwa wani abu mai kamar wannan zai iya faruwa ba ga wani tsohon shugaban Amurka ba," ya rubuta.

Ya ƙara da cewa: "Haƙiƙa wannan rana ce mai cike da baƙin tarihi ga Amurka. Muna cikin ƙasar da take komawa baya cikin sauri, amma tare (da ku), za mu sake Mayar da Amurka Gawurtacciyar Ƙasa."

Lauyan Mista Trump, Jim Trusty, ya shaida wa CNN cewa tsohon shugaban ya samu cikakkun bayanai game da tuhume-tuhumen a cikin takardar sammaci.

A cewarsa, tuhume-tuhumen sun haɗar da na haɗa baki da kalaman ƙarya da yi wa shari'a tarnaƙi, da kuma riƙe wasu bayanan sirrin ƙasa ba bisa ƙa’ida ba a ƙarƙashin dokar leƙen asiri.

Ma'aikatar Shari'a (DOJ) dai ta ƙi cewa uffan kuma ba a fitar da tuhumar a bainar jama'a ba.

Tuhumar hukuma (indictment), wata takardar shari'a ce da ke ƙunshe da cikakkun bayanai game da tuhume-tuhumen da ake yi wa mutum, tare da tabbatar da sanar da shi game da zargin manyan laifukan da ake cewa ya aikata.

Jami'an leƙen asiri za su gana da ma’aikatan Trump da jami’an tsaronsa domin tsara yadda zai tafi zuwa kotun Miami.

Wani mai shigar da ƙara na musamman Jack Smith yana nazarin shaidun da ke cikin shari'ar tun lokacin da babban mai gabatar da ƙara Merrick Garland ya naɗa shi don bincika wannan batun a watan Nuwamba.

A bara, an binciki gidan shakatawar Mista Trump na Florida wato Mar-a-Lago kuma an gano wasu takardun sirrin ƙasa 11,000, ciki har da kusan 100 da aka kebe. Wasu daga cikin waɗannan an yi musu lakabi da babban sirrin ƙasa.

Akwai rahotanni a makon jiya cewa masu gabatar da ƙara sun samu wani sautin muryar Trump wanda a ciki ya amince da ci gaba da riƙe wata takardar sirri bayan ya bar fadar White House a watan Janairun 2021.

Lamari da ya saɓa wa dokar Amurka, wani jami'in gwamnatin tarayya - ciki har da shugaban ƙasa - ya fita da ko kuma ya ajiye wasu bayanan sirrin ƙasa a wani wuri maras izini.

Masana harkokin shari'a sun ce har yanzu Mista Trump zai iya shiga takarar shugaban ƙasa.

David Super, farfesa a Cibiyar Shari'a ta Jami'ar Georgetown ya ce "Za a iya tuhumarsa a kowanne lokaci kuma hakan ba zai hana shi tsayawa takara ba."

Mista Super ya lura cewa Mista Trump na iya ci gaba da takara ko da an same shi da laifi.