BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023

Source: BBC

Ƙalubale shida da ke gaban sabbin hafsoshin tsaron Najeriya

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

A ranar Litinin ne, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kori dukkan manyan hafsoshin tsaron ƙasar, kuma ya maye guraben da wasu sababbi.

Wannan na cikin sauye-sauyen da shugaban ƙasar ke gudanarwa a ƙoƙarinsa na kafa sabuwar gwamnati.

Yayin da wasu masana ke ganin cewa sabbin hafsoshin da aka naɗa kan muhimman muƙaman tsaron suna da ƙwarewar da ta dace, ana ganin cewa akwai manyan ƙalubale a gabansu.

An naɗa sabbin jami'an ne a daidai lokacin da Najeriya take fama da ɗumbin matsalolin tsaro a cikin gida, kama daga rikicin 'yan a-ware da na 'yan ta-da-ƙayar-baya da rikicin 'yan fashin daji da matsalar garkuwa da satar mutane don neman kuɗin fansa da rikice-rikicen ƙabilanci da rikicin manoma da makiyaya da sauransu.

Mun yi duba kan manyan ƙalubalen da waɗannan sabbin jagorori a fagen tsaro za su yi arba da su, da zarar an tabbatar da naɗinsu.

Satar ɗanyen man fetur

Ɗanyen man fetur ne, babbar hajar da Najeriya take fitarwa zuwa ƙasashen waje, kuma ɗaya daga cikin ginshiƙan tattalin arziƙin ƙasar.

Mafi yawan kuɗin shigar da Najeriya ta dogara da shi, na fitowa ne daga man fetur.

Hakan ta sa satar ɗanyen man fetur ya zama babbar matsala ga Najeriya.

Rukunin haramtattun bututan man fetur da jami'an tsaron Najeriya ke ganowa, na ƙara fito da girman matsalar satar man a fili - lamarin na da ban al'ajabi hatta ga mazauna Neja-Delta, yankin da ya fi ƙaurin suna wajen satar man.

A jihar Delta, ɓarayin mai sun shimfiɗa bututu mai tsawon kilomita 4 har zuwa Tekun Atalantika mai tsananin tsaro.

A can ne manyan jiragen ruwa masu tsawon ƙafa 24 ke yin lodin mai na sata.

Ɗanyen man da ƙasar ke haƙowa ya ragu daga ganga miliyan 2.5 a kowacce rana a 2011 zuwa ƙasa da ganga miliyan ɗaya a ƙarshen 2022, in ji NNPC.

Lamarin da ya sanya har Najeriya ta koma ta biyu a jerin ƙasashe masu fitar da man fetur a Afirka.

Hukumomi sun ce an yi asarar fiye da dala biliyan 3.3 sakamakon satar mai a 2021 a daidai lokacin da sauran ƙasashe masu arzikin man fetur ke samun maƙudan kuɗi, ita kuwa Najeriya ba ta iya cimma adadin da aka ƙayyade mata ba.

Matsalar satar ɗanyen man fetur na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ake ganin matuƙar aka magance ta, za ta iya sauya rayuwar al'ummar ƙasar.

A makon jiya, shahararren tsohon jagoran tsagerun Neja-Delta, Asari Dokubo, ya zargi sojojin ƙasar da hannu wajen satar ɗanyen mai, duk da yake sun fito daga baya sun musa.

Idan zargin na Dokubo Asari ya zama gaskiya, kuma gwamnatin Bola Tinubu ta ɗaura aniyar magance matsalar, sabbin hafsoshin tsaron sai sun yi ƙoƙarin bankaɗowa da kakkaɓe manyan sojojin da ke da hannu a irin wannan badaƙala.

'Yan a-ware

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke addabar Najeriya a halin yanzu akwai rikicin 'yan a-ware musamman daga ƙungiyar IPOB masu rajin kafa ƙasar Biafra a yankin Kudu maso Gabas.

Mayaƙan ESN na Ƙungiyar IPOB a ƙarƙashin jagorancin Nnamdi Kanu ta ƙaddamar da hare-hare a kan jami'an tsaro da cibiyoyin gwamnati, sannan ta ayyana matakin hana fita duk ranar Litinin a wasu jihohin ƙabilar Igbo don ƙara matsin lamba ga hukumomin ƙasar.

Kama Nnamdi Kanu da gurfanar da shi gaban kotu bisa tuhume-tuhumen da suka shafi cin amanar ƙasa da ta'addanci sun sanya ƙungiyar wajen ƙara ƙaimi a hare-haren da take kai wa.

An zargi mayaƙan IPOB da hallaka mutane da dama ciki har da wasu fitattun 'yan siyasa da far wa ofisoshin hukumar zaɓe da ƙona ofisoshin 'yan sanda da sauransu.

A tsakiyar watan Maris ma, wasu sun zargi mayaƙan ƙungiyar da kai hari a kan kwambar motocin jami'an ofishin jakadancin Amurka a jihar Anambra, inda suka kashe wasu ma'aikatan ofishin.

Ƴan fashin daji

Wata matsalar tsaron da kuma ta fi addabar Najeriya, ita ce ta ƙungiyoyin ƴan fashin daji da suka fi harkoki a yankin arewa maso yamma da arewa maso tsakiyar Najeriya.

Tsawon shekaru, ƴan bindigar sun riƙa addabar musamman ƙauyuka da wasu garuruwa a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sokoto.

Haka lamarin yake a Neja da Kebbi har ma da jihar Kogi.

Gungun 'yan fashin da ke kai hari a kan babura suna far wa mutane da kashe-kashe, su raunata wasu sannan su sace mutane har sai an biya kuɗin fansa. Haka zalika, sun yi ƙaurin suna wajen ƙona garuruwa da tilasta wa mutane barin muhallansu.

Wannan matsala ta zamo babbar barazana, da ke neman durƙusar da harkar noma a irin waɗannan jihohi.

A halin da ake ciki manoma a yankunan da ke fama da rikicin 'yan fashin daji, ba su da tabbas kan yadda za ta kasance a daminar bana, don kuwa ƴan bindigan sukan hana jama'a sakat.

A kwanakin baya ma, 'yan bindigan sun sace mutane waɗanda yawancinsu yara ne kimanin 80 a jihar Zamfara, lokacin da suka je gyaran gona daf da faɗuwar damina.

Gyauron Boko Haram

Duk da yake, dakarun sojin Najeriya sun yi matuƙar rage ƙarfin ƙungiyar Boko Haram, wadda take gudanar da ayyukanta a arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu mayaƙan ƙungiyar suna iya ƙaddamar da miyagun hare-hare.

Tun a shekarar 2002 ne ayyukan Boko Haram suka fara ƙamari a ƙasar, lamarin da ya raba miliyoyin al'umma da muhallansu, yayin da rikicin ya yi sanadin rasuwar dubban mutane.

Boko Haram ta yi ƙaurin suna wajen satar ɗalibai 'yan mata daga makarantarsu ta sakandire, sannan an zarge ta aikata miyagun kashe-kashe na rashin imani.

Ayyukan ƙungiyar sun fi ƙazancewa ne a lokacin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yayin da gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi iƙirarin cewa ta yi nasarar daƙile ayyukanta.

Amma a wani taro kan harkokin tsaro da aka yi kwanan nan a Amurka ya bayyana yadda mayaƙan ƙungiyar ke daɗa rungumar fasahar zamani wajen gudanar da lamurransu.

Al'amarin da zai iya haifar da barazana ga tsaron ƙasar.

Daya daga cikin manyan ƙalubalen da sababbin hafsoshin za su fuskanta shi ne nemo dabarun daƙile sabbin dabarun zamani da mayaƙan Boko Haram ke ƙoƙarin amfani da su wajen ci gaba da kai hare-hare.

Wasu daga cikin irin waɗannan abubuwa su ne amfani da ƙananan jirage maras matuƙa.

Walwalar ƴan sanda

Ba sabon abu ba ne, yadda jami'an ƴan sanda ke kokawa a kan rashin gwaɓin albashi da walwala.

Akasarin barikokin ƴan sandan ƙasar na cikin mummunan yanayi, sannan darajar jami'an hukumar ƴan sandan ta yi rauni a idanun al'umma.

Wannan ya haifar da tazgaro a ƙoƙarin tabbatar da tsaro a cikin ƙasar.

Ana ganin cewa babbar matsalar da ke addabar rundunar ƴan sanda ta Najeriya ita ce rashin isassun kuɗi.

Babu ƙwaƙƙwarar hanyar bibiyar halin da ƴan sandan ke ciki da kuma sauraron ƙorafe-ƙorafensu.

Haka kuma, akwai zarge-zargen aikata cin hanci da rashawa da suka yi katutu a aikin na ƴan sanda, tun daga wajen ɗaukar aiki da ƙarin girma da canjin wurin aiki.

Ana ganin cewa magance wannan matsalar na buƙatar komawa tushe ta hanyar samar da isassun kuɗi ga rundunar da kawar da rashawa da kuma rungumar dabarun tsaron al'umma na zamani.

Tattara bayanan tsaro

A kwanan baya, an jiyo Shugaba Tinubu da kansa yayin wata ziyara zuwa sabon ofishin Mai ba shi shawara kan harkar tsaro da cibiyar yaƙi da ta'addanci, ya bayyana cewa ba zai lamunci ci gaba da aiki tsakanin hukumomin tsaron ƙasar ba tare da haɗin kai ba.

Ya kuma yi gargaɗi a kan ɓoye bayanan sirri a tsakanin juna a ɓangaren hukumomin tsaron.

Masani kan tsaro Dr. Kabir Adamu ya ce rahoton wani binciken da suka gudanar kuma suka miƙa wa shugaban ƙasa ya nuna cewa, ɗaya daga cikin manyan kalubalen da harkar tsaron Najeriya ke fuskanta shi ne rashin tattara sahihan bayanan sirri, da tantance su, da kuma aiki da su yadda ya kamata.

Ya ƙara da cewa kowane bangare a cikin bangarorin tsaron ƙasar 27 yana fama da wannan matsalar, don haka, akwai bukatar mai bai wa shugaban ƙasa shawara a harkar tsaro ya bi diddigin wannan batu kuma ya sanya ido don tabbatar da samun mafita.

Baya ga waɗannan manyan matsalolin akwai kuma wasu da ake ganin suna kawo cikas sosai a harkar tsaron ta Najeriya.

Ɗaya daga ciki, ita ce zagon ƙasan ƴan siyasa waɗanda ke kawo nakasu a harkar ta tsaro.

Sau da dama tsoma bakin ƴan siyasa ta hanyar sawa ko hanawa kan haifar da matsaloli da dama.

Sai kuma batun rashin ladaftarwa a kan jami'an da suka saɓa ƙa'ida ko suka yi sakaci wajen tafiyar da ayyukansu.

A yanzu haka dai al'ummar Najeriya za su zura ido domin ganin kamun ludayin waɗannan sababbin manyan hafsoshi da aka naɗa.

Musamman ganin yadda aka zargi magabatansu da gazawa.

Shin ko waɗanne sabbin dabarun yaƙi da matsalar tsaro za su zo da su?