An sanar da waɗanda suka lashe gasar ɗaukan hoto ta duniya ta 2023, wadda kamfanin Sony ya ɗauki nauyi, inda mai ɗaukan hoto Edgar Martins na Portugal ya zama zakara bisa hotunan da ya ɗauka na yankunan da ake yaƙi.
Martins ya ɗauki hotunan ne a matsayin karramawa ga abokinsa mai ɗaukan hoto, Anton Hammerl, wanda aka kashe a lokacin yaƙin da aka yi a Libiya a 2011.
Bayan lashe gasar, Martins ya ce "Wannan ba ƙaramar karramawa ba ce a zaɓe ka - kasancewar akwai sama da da mutum 180,000 wadanda suka shiga gasar, wannan abin girmamawa ne."
Hotunan Martins sun yi zarra ne a ɓangare ɗaukan hoton Portraite.
Nan ƙasa akwai saurarn waɗanda suka yi zarra a wasu ɓangarorin, da kuma tsokacin da suka yi.
Zane
Kamfanin siminti wanda Fan Li daga China ya ɗauka
"Kamfanin siminti na Tieshan yana a birnin Guilin ne na yankin Guangxi, a kudancin China.
"An gina kamfanin ne a 1996 kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin Guilin da kuma samar da gine-gine a birnin.
"Sai dai kasancewar an gina kamfanin ne a kusa da rafin Li, yanzu an ɗauke kamfanin zuwa wani wuri, inda aka bar tsofaffin gine-gine, da wuraren iyo da kuma hanyoyin jirgin ƙasa."
Basira
The Right to Play na Lee-Ann Olwage daga Afirka ta Kudu
"Wanna hoto ya nuna yadda za a iya ƙarfafa wa yara mata gwiwa ta hanyar raha.
Muhalli
Miruku na Marisol Mendez da Federico Kaplan daga Bolivia da Argentina
Sarari
Event Horizon na Kacper Kowalski daga Poland
Wasanni
Mace mai wasan Baseball wadda ta yi nasara a gasar maza - na Al Bello daga Amurka
Dabbobi
Namun dawa a birni na Corey Arnold daga Amurka
Sauran hotuna