BBC Hausa of Sunday, 11 June 2023

Source: BBC

‘Yadda kasuwar masu gyaran talakmi ta bude bayan cire tallafin mai’

Wani mai sana'ar gyaran takalma na jihar Kano Wani mai sana'ar gyaran takalma na jihar Kano

Wasu masu sana'ar gyaran takalma na jihar Kano da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya sun ce kasuwarsu ta bude kuma ribar da suke samu ta karu saboda sun ce mutane na tafiya mai nisa a kafa saboda tsadar man fetur.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da guna-guni kan cire tallafin mai da gwamnatin kasar ta yi a baya-bayan nan da ke sa gidajen mai ke siyar da mai a kan Naira 600 kan kowace lita a wasu wurare.

Wannan lamari ya sa wasu mutane sun jingine motoci da baburansu don yin amfani da abubuwan hawa na haya yayin da wasu masu karamin karfi ke takawa a kafa.

Babura masu kafa uku da ake kira Keke napep wadanda su aka fi amfani da su wurin sufuri kuma masu sufuri da ita sun ce kara kudin da su ke karba daga fasinja ya zama dole saboda tashin farashin man fetur.

Kudin zirga-zirga a cikin birnin Kano ya rubanya sau uku tun bayan cire tallafin, a inda wuraren da akan je a kan N100 yanzu sai an biya tsakanin N250 zuwa N300 a wasu wurare.

Wannan shi ya sa mutanen da ba su iya biyan wadannan kudaden ke tafiya a kafa idan wurin da za su je ba shi da nisa sosai.

Muhammad Auwalu, wanda ke gyaran takalmi a kan titin Zoo road ya shaida wa BBC cewa kasuwarsu ta bude matuka cikin 'yan kwanakin nan.

''Kwarai da gaske kasuwar mu ta bude sosai a halin yanzu kuma hakan ya kasance ne saboda mutane na takawa a kafa sosai yanzu kuma hakan ya na sa talakma su yi dauda ko su kece''

''Wani lokaci mutane har layi su ke yi a gaba na suna jiran in yi masu aiki, ba haka ya ke kafin a cire tallafin mai ba''

''Yadda na ke yi da mutane shi ne, idan akwai wanda ya ke sauri ya na iya rokon wanda ya riga shi zuwa saboda in fara yi masa gyara ko wanke masa takalma''

Muhammad ya kara da cewa, ba wai yana farin cikin halin da ake ciki ba ne yanzu amma dai haka rayuwa ta ke, yayin da wasu ke bakin ciki akwai wadanda ke amfana da lamarin.

'Suna rububin mu'

Wani mai gyaran takalmi mai suna Sani Tukuntawa ya ce duk da bunkasar da kasuwarsu ta yi, ba su da niyyan kara kudin aikin su.

''Ba mu son kara wa mutane nauyi bayan wanda ke kan su yanzu, mun san cewa jama'a n cikin wani hali yanzu kuma duk da cewa su na rububin mu a halin yanzu ba mu da niyyan kara kudin da mu ke karba kan ayukan mu.

Sani, ya kara cewa ingancin takalman da mutane ke amfani da su yanzu ya ragu sosai shi ya sa su ke da saukin lalacewa daga an dan yi amfani da su.

''Kwanakin baya ne takalma ke da inganci, amma yanzu ingancin ya ragu shi ya sa daga an dan taka da su kadan sai an yi masu gyara.''

Da Muhammad da Sani sun ce su na fatan cewa nan ba da jimawa ba 'yan Najeriya samu walwala kuma matsalolin da ake fuskanta za su kare.

Wane ne ya cire tallafin man fetur?

Shugaban Najeriya na biyar tun bayan komawar mulkin dimokradiyya a 1999, ya kawo karshen tallafin man fetur wanda aka kwashe shekaru da dama ana biya, a lokacin da ya bayyan cewa "tallafin man fetur ya kare," a jawabin rantsar da shi ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Dan siyasan mai shekara 71 da haihuwa bai bada wani wa'adin lokaci ko tsarin da zai bi don cire tallafin ba amma ya ce abu ne da zai gudana a hankali,

Sa'o'i kadan bayan jawabin Tinubu, daruruwan mutane su ka nufi gidajen mai da motoci ko kuma dauke da jarkoki domin siyan mai.

Mutane kalilan ne su ka yi sa'ar siyan man fetur a lokacin domin mafi yawancin gidajen sun yi ikirarin cewa man su ya kare.

Tawagar shugaban ta fito ta fayyace cewa janye tallafin ba zai fara aiki ba har sai karshen watan Yuni kamar yadda kasafin kudin gwamnati mai barin gado ta tanadar.

Amma wannan jawabin ya kasanec ihu bayan hari don kuwa hankalin mutane ya riga ya tashi.

Kuma ya zuwa ranar Laraba, da ya tabbata cewa gwamnati ta daina bayar da tallafin sai kamfanin man fetur na kasar NNPCL ya ba da sanarwar cewa zai kara farashin man fetur.